"Abun Takaici Ne": Sylva Ya Caccaki Jonathan Bisa Kalamansa Kan Zaben Gwamnan Bayelsa
- Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Timipre Sylva, ya mayar wa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan martani kan kalaman da ya yi kan sakamakon zaɓen Bayelsa
- Sylva ya ce kalaman Jonathan abin takaici ne amma yana son ya yarda cewa an yi kuskuren maganar tsohon shugaban ne
- Jonathan a ziyarar da ya kai wa Gwamna Duoye Diri ya ce da ya mayar da mahaifiyarsa Abuja da dan takarar PDP ya sha kaye a hannun Sylva
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Yenagoa, jihar Bayelsa - Ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Bayelsa, Timipre Slyva, ya caccaki tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, kan kalaman da ya yi dangane da sakamakon zaɓen gwamnan da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Sylva ya bayyana kalaman Jonathan na cewa zai mayar da mahaifiyarsa Abuja da Gwamna Duoye Diri ya sha kaye a hannun ɗan takarar APC a matsayin abin takaici.
Sai dai, tsohon ƙaramin ministan albarkatun man fetur, ya ce yana so ya yarda cewa an yi kuskuren maganar Jonathan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake mayar da martani ga kalaman Jonathan ta shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) @HETimipreSylva, ya bayyana cewa:
"Maganar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan abin takaici ne. Ina fata da gaske an yi kuskuren ambato kalamansa. Bari kawai na faɗi abin da mai girma Wole Soyinka ya faɗa, "Za ku iya fitar da ɗigon ruwa daga cikin fadama amma ba za ku iya fitar da fadama daga cikin ɗigon ruwa ba."
Dalilan da suka sanya Sylva ya sha kaye
Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a zaɓen jihar Bayelsa, Timipre Sylva, ya yi rashin nasara a hannun Gwamna Duoye Diri na jam'iyyar PDP.
Zaɓen mataimakin da Sylva ya yi da goyon bayan da Goodluck Jonathan ya nuna ga Duoye Diri sun taka rawar gani wajen rashin nasarar Timiprw Sylva.
Sylva Bai Ziyarci Gwamna Diri Ba
A wani labarin kuma, an tabbatar da cewa bidiyon da aka yi ta yaɗa wa kan cewa Timipre Sylva ya ziyarci Gwamna Duoye Diri bayan rashin nasararsa a zaɓen gwamnan Bayelsa.
Bincike ya nuna cewa bidiyon an ɗauke shi ne watanni kusan shida kafin a gudanar da zaɓen gwamnan jihar na ranar. Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023.
Asali: Legit.ng