Kotun Daukaka Kara Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Karar da Ke Neman Tsige Gwamnan PDP a Arewa
- Kotun ɗaukaka ƙara ta sanya ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba a matsayin ranar yanke hukunci kan shari'ar gwamnan Plateau
- Ɗan takarar APC Nentawe Yilwatda ya garzaya kotun ne bayan kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta tabbatar da nasarar Gwamna Mutfwang na PDP
- Masu ruwa na jam'iyyun biyu sun nuna ƙwarin gwiwar cewa za su yi nasara a hukuncin da kotun za ta yanke yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - A yau ne kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja za ta yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar Plateau.
Kotun za ta yanke hukunci ne tsakanin Gwamna Caleb Mutfwang na jam'iyyar PDP da ɗan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Dr Nentawe Yilwatda, cewar rahoton jaridar Blueprint.
Tun da farko dai kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta tabbatar da zaɓen Gwamna Mutfwang, amma ɗan takarar APC ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata sanarwar da jaridar Daily Trust ta ci da ita a ranar Asabar ta ce "An tsayar da ranar 19 ga watan Nuwamba da ƙarfe 12:00 na rana domin yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar"
Me ƴan PDP, APC ke cewa kan shirin yanke hukuncin?
Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP da APC na bayyana ƙwarin gwiwar samun nasara gabanin yanke hukuncin.
Wani shugaban jam’iyyar PDP na yankin Plateau ta Kudu, Simon Venmak Gomla, ya ce yana da yaƙinin samun nasara a kotun ɗaukaka ƙara duk da hukuncin da aka yanke a baya kan ƴan majalisar wakilai na jam'iyyarsu.
Shi ma sakataren yaɗa labaran jam'iyyar APC na jihar, Sylvanus Namang, ya bayyana ƙwarin gwiwar samun nasara a kotun ɗaukaka ƙara, inda ya ƙara da cewa PDP yaudarar kanta kawai ta ke yi idan ta yi tunanin samun nasara.
Mutfwang Ya Magantu Kan Hukuncin Kotun Zaɓe
A wani labarin kuma, Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau, ya nuna farin cikinsa kan nasarar da ya samu a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar.
Gwamnan wanda ya yaba da hukuncin kotun zaɓen ya bayyana cewa hukuncin ya nuna cewa shari'a ta yi magana da babbar murya.
Asali: Legit.ng