Hukuncin Kotun Daukaka Kara: Farfesan Arewa Ya Yi Gargadi Kan Yiwuwar Barkewar Rikici a Kano

Hukuncin Kotun Daukaka Kara: Farfesan Arewa Ya Yi Gargadi Kan Yiwuwar Barkewar Rikici a Kano

  • Kotun daukaka kara ta soke zaben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a Abuja a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba
  • Kotun ta riki cewa dan takarar na jam'iyyar NNPP, a zaben gwamna na watan Maris, Gwamna Yusuf, bai cancanci yin takara a zaben ba
  • Hukuncin kotun daukaka karar ya haifar da martani daban-daban, kuma Farfesa Farooq Kperogi ya tsoma baki a ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kano, jihar Kano - Farfesa Farooq Kperogi, haifaffen dan jihar Kwara mazaunin Amurka, ya soki hukuncin kotun daukaka kara da ya tabbatar da tsige Gwamna Abba Yusuf.

Kperogi, a cikin wallafarsa a ranar Asabar, 18 ga Nuwamba, ya ce "yana fatan wannan cin zarafi da aka yi kan gaskiya ba shine tartsatsin da zai kunna wutar rikici ba a Kano - da kasar."

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya yi zazzafan martani kan hukuncin kotun daukaka kara na sauke Abba Gida-Gida

An yi gargadi kan yiwuwar barkewar rikici saboda tsige Abba Gida Gida
Hukuncin Kotun Daukaka Kara: Farfesan Arewa Ya Yi Gargadi Kan Yiwuwar Barkewar Rikici a Kano Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, Rabiu Musa Kwankwaso, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Rikicin siyasa na ci gaba da gudana a Kano

Marubucin ya yi zargin cewa Abdullahi Ganduje, shugaban jam'iyyar APC mai mulki na kasa, "yana amfani da kotuna a matsayin yan baranda don yakar Rabiu Kwankwaso".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben watan Fabrairu. A daya bangaren kuma, Ganduje ne tsohon gwamnan jihar Kano da ya mika mulki. Tsigaggen gwamnan Kanon dan NNPP ne kuma dan gidan Kwankwaso.

Kperogi, a cikin rubutunsa na baya-bayan nan, ya bayyana nasarar da Gwamna Yusuf ya samu a zaben da aka gudanar a farkon wannan shekarar (2023) a matsayin "wanda aka samu bisa tsarin doka" yayin da ya zargi APC da kokarin "sace" shi daga hannunsu.

Ya rubuta:

"Kamar yadda na nuna a shafina a ranar 23 ga watan Satumba, 2023, mai taken "Dalilin da yasa hukuncin Kano ba zai yi tasiri ba," a bayyane yake cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa a yanzu, Abdullahi Ganduje ya kuduri aniyar jajircewa ta kowani hali tare da amfani da karfin gwamnatin tarayya da ke tafin hannunsa don kwace mulkin da jam’iyyarsa da jiga-jigansa suka rasa a hannun Rabiu Kwankwaso da sirikinsa a zaben gwamna.”

Kara karanta wannan

"Yan maula sun fara": Jama’a sun yi caaa kan Ali Nuhu bayan ya taya Gawuna murnar nasara a kotun

Kperogi ya kara da cewar:

"Shawarata ga Shugaban kasa Tinubu shine ya zuba idanu sosai saboda wannan yanki ne mai hatsarin gaske. Fushin gaske kan rashin adalci - a kan azabar da ake ci gaba da dandanawa a kasar - na iya haifar da tashin hankali wanda ba za mu iya hasashen abun da zai faru ba."

Legit Hausa ta ji ta bakin wani mai bibiyar harkokin siyasar Kano mai suna mallam Hassa Abdullahi don ta bakinsa game da gargadin da Farfesa Kperogi ya yi inda ya ce:

“Shakka babu kwace kujerar Gwamna Abba Kabir Yusuf zai iya tayar da tarzoma a jihar Kano. Kowa ya san Kanawa Abba suka yi amma saboda wani dalili na son zuciya an dage sai an murde gaskiya ta karfi da yaji.
“Karara a bayyane yake cewa Ganduje yana amfani da damar yake da ita a matsayinsa na shugaban jam’iyya mai mulki a kasar wajen yakar abokin hamayyarsa a siyasa wato Kwankwaso, kuma yana ganin sai ya daddake Abba daga kujerarsa ne zai zama ya yi galaba a kansa.

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamnan Kano, Malamin addini ya yi hasashen sakamakon hukuncin zaben Kaduna da Nasarawa

“Yanzu da ake maganar shiga kotun koli, ina kira ga bangaren shari’a da ta tsaya tsayin daka don ganin ta warware rashin adalcin da aka yi saboda wanzuwar zaman lafiya da ra’ayin Kanawa.”

Ali Nuhu ya taya Gawuna murna

A wani labarin, mun ji cewa fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Ali Nuhu, wanda aka fi sani da sarki ya yi martani bayan kotun daukaka kara ta tabbatar da Nasir Yusuf Gawuna a matsayin zababben gwamnan Kano na 2023.

A ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamba ne, kotun daukaka kara mai zama a Abuja ta tsige gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da soke nasarar zabensa na ranar 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng