Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Bayyana Matakin Dauka Na Gaba Bayan Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Shi

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Bayyana Matakin Dauka Na Gaba Bayan Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Shi

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano bai gamsu da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ba na tsige shi
  • Gwamnan ya umarci lauyoyinsa da su fara shirin ɗaukaka kan ƙara kan hukuncin a kotun ƙoli
  • Gwamnan ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa kotun ƙoli za ta warware hukuncin ƙananan kotun wanda ya kira a matsayin rashin adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce ya sanar da lauyoyinsa da su garzaya zuwa kotun ƙoli dangane da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke, cewar rahoton The Cable.

A ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba ne kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano ta yanke.

Kara karanta wannan

"Alhakin rusau ne" Shugaban jam'iyya na Kano ya maida martani mai ɗumi kan tsige Abba Gida-Gida

Gwamna Abba ya garzaya kotun koli
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tafi kotun koli Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Kotun ta tsige Yusuf ɗan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a matsayin gwamnan jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi ga al’ummar jihar a ranar Asabar, gwamnan na Kano ya bayyana hukuncin kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara a matsayin “rashin adalci".

Wane fata Gwamna Abba yake yi?

Yusuf ya ce yana da kwarin gwiwar cewa kotun ƙoli za ta yi watsi da hukunce-hukuncen ƙananan kotunan.

A kalamansa:

“Ina so in sanar da mutanen Kano nagari da kuma ƴan Najeriya masu kishin kasa cewa bisa amincewar masu ruwa da tsakinmu, mun umurci lauyoyinmu da su fara shirin ɗaukaka ƙara kan wannan hukuncin a kotun ƙoli."
“Muna da ƙwarin gwiwar cewa kotun ƙoli da yardar Allah (SWT) za ta yi watsi da waɗannan kura-kurai na shari’a da kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yi, sannan ta sake tabbatar da nasarar mu wacce al'ummar jihar Kano suka ba mu."

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun dauki mataki a wasu wurare a Kano bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tsige Gwamna Abba

Gwamnan na Kano ya buƙaci al'ummar jihar da su cigaba da gudanar da sana’o’insu na yau da kullum, inda ya ƙara da cewa an ɗauki matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.

Ya ƙara da cewa wannan koma baya na ɗan lokacin ba zai hana gwamnatinsa cigaba da gudanar da ayyukan da ta ke yi ba.

Kotu Ba Ta Yi Wa Al'ummar Kano Adalci Ba, Cewar Gwamna Abba

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana cewa kotun ɗaukaka ƙarar ba ta yi wa al'ummar jihar Kano da jam'iyyar NNPP adalci ba a hukuncin da ta yanke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng