Kano: Mu Hadu a Wasan Karshe, Ganduje Ya Yi Zazzafan Martani Ga Abba Gida Gida

Kano: Mu Hadu a Wasan Karshe, Ganduje Ya Yi Zazzafan Martani Ga Abba Gida Gida

  • Shugaban jami'yyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Ganduje ya sha alwashin yin kaca-kaca da jam'iyyar NNPP a kotun koli
  • Ganduje ya bayyana haka ne yayin da ya ke martani kan hukuncin kotun koli a yau Juma'a 17 ga watan Nuwamba
  • Shugaban APC ya ce babu matsala don sun je kotun koli amma ya ce su na jiransu a can don kara ba su kashi a babbar kotun

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya ce akwai tabbacin za su sake nakasa NNPP a kotun koli.

Ganduje ya bayyana haka ne yayin da ya ke martani kan hukuncin kotun da aka yanke a yau Juma’a 17 ga watan Nuwamba, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamnan Kano, Malamin addini ya yi hasashen sakamakon hukuncin zaben Kaduna da Nasarawa

Ganduje ya yi martani kan hukuncin kotu a zaben jihar Kano
Ganduje ya yi zazzafan martani ga Abba Gida Gida. Hoto: Ganduje Umar.
Asali: Facebook

Mene Ganduje ke cewa kan shari'ar Kano?

Ya ce ya ji dadin wannan hukunci na kotu kuma ya tabbata Abba Kabir zai sake daukaka kara inda ya ce za su sake karban kaya a kotun koli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam’iyyar ya bayyana haka ne ga manema labarai a Abuja a yau Juma’a 17 ga watan Nuwamba, cewar Leadership.

Ya ce:

“Babu wata matsala don sun je kotun koli, mu na jiransu a kotun koli kuma In shaa Allah za mu yi nasara a kansu.”

Wane hukunci kotun ta yanke a Kano?

Wannan martani na Ganduje na zuwa bayan kotun daukaka kara ta sake tabbatar da kwace kujerar Abba Kabir na jam’iyyar NNPP a matsayin gwamna.

Kotun ta kuma sake tabbtar da nasarar Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Wane hali ake ciki a birnin bayan kwace kujerar Abba Kabir da kotun daukaka kara ta yi?

Halin da Kano ke ciki bayan yanke hukunci

A wani labarin, yayin da aka yanke hukuncin zaben gwamnan jihar Kano a yau Juma’a, mutane sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

An tsaurara tsaro ko ina a birnin don tashin husuma da zai biyo baya yayin da ake yanke hukuncin zaben.

Amma sabanin haka an gano mutane su na ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata matsala ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.