Kano: Wane Hali Ake Ciki a Birnin Bayan Kwace Kujerar Abba Kabir da Kotun Daukaka Kara Ta Yi?

Kano: Wane Hali Ake Ciki a Birnin Bayan Kwace Kujerar Abba Kabir da Kotun Daukaka Kara Ta Yi?

  • Yayin da aka yanke hukuncin zaben gwamna a Kano, mutane sun ci gaba da harkokinsu kamar yadda ya dace
  • Abin da ba a yi tsammani ba yayin da kowa ke gudanar da al'amuranshi na yau da kullum ba tare da wata matsala ba
  • Wannan na zuwa ne bayan rusa zaben Gwamna Abba Kabir da kotun daukaka kara ta sake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - A yau Juma'a 17 ga watan Nuwamba aka yanke yanke hukuncin zaben gwamnan jihar Kano.

Yayin hukuncin, kotu ta sake tabbatar da hukuncin karamar kotu da ta rusa zaben Gwamna Abba Kabir na jihar Kano.

Halin da ake ciki a birnin Kano bayan hukuncin kotun daukaka kara
Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan zaben jihar Kano. Hoto: Abba Kabir, Nasiru Gawuna.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a Kano?

Kara karanta wannan

'Jarabawa ce, gwamna ya yi martani kan hukuncin kotun da ta rusa zabenshi, ya sha alwashi

Har ila yau, kotun ta sake tabbatar da Nasiru Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da sake rusa zaben Gwamna Abba Kabir, birnin Kano ya kasance babu wani tashin hankali saboda hukuncin kotun.

Wakilin Punch ya ruwaito cewa kowa na gudanar al'amura na yau da kullum babu wani tashin hankali, The Discover ta tattaro.

Wane yanayi mutane su ke a Kano?

Har ila yau, akwai zirga-zirgar ababan hawa a birnin kamar babu wani abu da ya faru na hukuncin kotun.

Jami'an tsaro kuwa an watsa su ta ko wane lungu da sako na jihar don tabbatar da doka da samar da zaman lafiya a birnin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kasuwanni da gidajen mai da sauran lmuran yau da kullum na ci gaba da tafiya ba tare da wata cikas ba.

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya bayan kotun daukaka kara ta tsige Abba Gida-Gida daga matsayin gwamnan Kano

Legit Hausa ya ruwaito a jiya cewar jam'iyyun da suke shari'ar guda biyu sun sanya hannu don zaman lafiya inda suka roki magoya bayansu da su kai zuciya nesa.

Shugabannin jam'iyyun sun yi wannan yarjejeniya ce a babban ofishin 'yan sanda da ke Kano a jiya Alhamis 16 ga watan Nuwamba.

Kotu ta sake tabbatar da hukuncin kotun zabe a yau

A wani labarin, kotun daukaka kara ta sake kwace kujerar Gwamna Abba Kabir na jihar Kano.

Kotun ta tabbatar da nasarar Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

A baya, kotun zabe ta rusa zaben Gwamna Abba Kabir na jam'iyyar NNPP saboda tafka kura-kurai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.