Zaben Kano: Hadimin Atiku Ya Bayyana Wanda Zai Samu Nasara a Kotun Ɗaukaka Kara
- Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Abdulrasheed Shehu, ya yi hasashen wanda zai samu nasara a Kotun ɗaukaka ƙara kan zaben Kano
- Jigon jam'iyyar PDP ya bayyana cewa lissafin da ke gaban APC shi ne ta maida Najeriya hannun jam'iyya ɗaya
- Kalaman Shehu na zuwa ne yayin da Kotun ɗaukaka kara ta shirya yanke hukunci kan sahihin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Kano yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Abdulrasheed Shehu, ɗaya daga cikin hadiman Atiku Abubakar, ya yi hasashen hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara zata yanke kan kujerar Gwamnan jihar Kano.
Shehu, mai magana da yawun Atiku ya ce Kotun ɗaukaka ƙara zata bai wa jam'iyyar APC nasara a hukuncin da zata yanke yau Jumu'a.
A cewarsa, tuni jam'iyyar APC ta fara kokarin sauya Najeriya zuwa ƙasa mai jam'iyya ɗaya kaɗai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wannan hasashe ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X watau Tuwita ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba.
A rubutun da ya wallafa, Jigon PDP ya ce:
"Kuma idan Allah ya kaimu gobe, za su kwace Kano, tsarin jam'iyya ɗaya ne ke tafe."
Yadda hukuncin Kotun zaɓe ya bar baya da ƙura
Hukuncin tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP wanda Kotun zaɓe ta yanke a watan Satumba, ya haddasa cece-kuce da martani mai tsaki daga masu ruwa da tsaki.
Har kawo yanzun manyan ƴan siyasa musamman waɗanda ke tsagin adawa suna nuna takaici dangane da wannan mataki na Kotun zabe.
A halin yanzu, Kotun ɗaukaka ƙara ta tsaida Jumu'a, 17 ga watan Nuwamva a matsayin ranar yanke hukunci wanda shi ne na ƙarshe a ƙarar da Abba ya ɗaukaka.
NNPP da APC Sun Sanya Hannu a Yarjejeniyar Zaman Lafiya
A wani rahoton na daban NNPP mai kayan daɗi da APC sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin da Kotun ɗaukaka ƙara ta shirya yanke hukunci kan zaben Kano
Kwamishinan yan sandan jihar, CP Gumel, ya ce sun ɗauki matakan tabbatar da zaman lafiya kafin, lokacin da bayan yanke hukunci.
Asali: Legit.ng