NNPP da APC Sun Sanya Hannu a Yarjejeniyar Zaman Lafiya Gabanin Hukuncin Kotu

NNPP da APC Sun Sanya Hannu a Yarjejeniyar Zaman Lafiya Gabanin Hukuncin Kotu

  • NNPP mai kayan daɗi da APC sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin da Kotun ɗaukaka ƙara ta shirya yanke hukunci kan zaben Kano
  • Kwamishinan yan sandan jihar, CP Gumel, ya ce sun ɗauki matakan tabbatar da zaman lafiya kafin, lokacin da bayan yanke hukunci
  • Kotun ɗaukaka ƙara ta tsaida gobe Jumu'a domin raba gardama tsakanin gwamna Abba na NNPP da Gawuna na APC

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP mai mulki da jam'iyyar APC sun rattaɓa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya yayin da Kotun ɗaukaka kara zata yanke hukunci kan zaɓen Gwamnan Kano.

Abba Kabir Yusufa da Yusuf Gawuna.
NNPP da APC Sun Sanya Hannu a Yarjejeniyar Zaman Lafiya Gabanin Hukuncin Kotu Hoto: Abba Kabir Yusuf, Dr Yusuf Gawuna
Asali: Facebook

Manyan jam'iyyun biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar a hedkwatar ƴan sandan Kano tare da alƙawarin zaman lafiya gabanin, lokacin da bayan hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Tinubu ya shiga babbar matsala kan tsige Gwamna Abba Gida-Gida

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kotun ɗaukaka ƙara ta tsaida ranar Jumu'a, 17 ga watan Nuwamba, 2023 a matsayin ranar da zata raba gardama tsakanin Abba da Gawuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan yan sanda reshen jihar, Mohammed Usaini Gumel, ya bayyana irin matakan da hukumar ta ɗauka yayin da yake jawabi a hedkwata da ke Bompai ranar Alhamis.

Ya ce hukumar ƴan sanda ta tsara hanyoyin da za su tabbatar da zaman lafiya a jihar kafin yanke hukunci da lokacin da kuma bayan yanke hukunci.

Gumel, wanda ya yi jawabi tare da rakiyar sauran shugabannin hukumomin tsaro, ya kara da cewa sun kammala dukkan shirye-shiryen tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

Yadda PDP da APC suka sa hannu kan yarjejeniya

Mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP, Wada Ibrahim, da sakataren jam’iyyar APC Ibrahim Sarina, ne suka wakilci jam’iyyun siyasar biyu a wurin taron.

Kara karanta wannan

Abba Vs Gawuna: Hadimin Atiku ya yi hasashe, ya faɗi wanda zai samu nasara a Kotun ɗaukaka kara

A ruwayar Daily Post, CP Gumel ya ce:

“Jam'iyyun biyu sun amince da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali su dore kafin, lokacin da kuma bayan ayyana hukuncin kotun daukaka kara."
"Shugabannin jam'iyyun biyu sun bamu tabbacin cewa za su isar da wannan sako ga mabiyansu da magoya baya."

Wasu mazauna Kano kuma mambobin NNPP sun faɗa wa Legit Hausa cewa wannan mataki na ƴan sanda abu ne mai kyau, kuma suna fatan a zauna lafiya.

Malam Sa'idu, jigon NNPP ya bayyana mana cewa ba abin da ke tafiya daidai idan babu zaman lafiya, ya kuma ƙara da addu'ar Allah ya bai wa Gwamna Abba nasara.

"A gaskiya hukumar ƴan sanda ta ɗauki matakai na tabbatar da tsaro a Kano bayan hukuncin Kotun ɗaukaka kara. An tsaurara matakan tsaro, muna fatan hakan ya yi aiki."

"Ina kuma rokon Allah ya tabbatar mana da nasarar mu, ina mamakin ga wanda ya ci zaɓe wanda Kanawa suka zaɓa amma ana neman kwace wa," in ji Sa'idu.

Kara karanta wannan

Tirƙashi: Yadda yaro ɗan shekara 9 ya yi garkuwa da ƴar shekara 5 a Bauchi

PDP ta rasa ɗan majalisa a Yobe

A wani rahoton na daban Jam'iyyar PDP ta rasa ɗan majalisa ɗaya tilo da take da shi a majalisar dokokin jihar Yobe ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba.

Musa Lawan Majakura, matashin da ya lallasa tsohon kakakin majalisar a PDP ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262