'Inconclusive': Kotu Ta Ayyana Zaben Gwamnan Zamfara a Matsayin Wanda Bai Kammala Ba, Za a Sake Zabe
- Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari’ar zaben gwamnan jihar Zamfara a yau Alhamis 16 ga watan Nuwamba
- Kotun ta ayyana zaben a matsayin wada bai kammala ba inda ta bukaci sake zabe a wasu kananan hukumomi uku
- Legit Hausa ta ji ta bakin wani jigon jam'iyyar APC kan wannan hukunci na kotu a zaben jihar Zamfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara – Kotun daukaka kara ta raba gardama kan shari’ar zaben gwamna jihar Zamfara, kamar yadda Channels TV ta tattaro.
Kotun da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba inda ta umarci sake zabe a kananan hukumomi guda uku.
Wane hukunci kotun ta yanke a zaben Zamfara?
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Maradun da Birnin Magaji da kuma karamar hukumar Bukuyun, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta yanke wannan hukunci ne a yau Alhamis 16 ga watan Nuwamba a Abuja inda ta yi fatali da hukuncin karamar kotun a baya.
Har ila yau, kotun ta bayyana cewa kotun sauraran korafe-korafen zabe ta yi kuskure wurin kin yin amfani da shaidun jam’iyyar APC.
Wane hukunci karamar kotu ta yanke?
Gwamna Dauda Lawal na jam'iyyar PDP ya yi nasara a karamar kotun da ta yanke hukunci a kwanakin baya.
Karamin Ministan Tsaro a yanzu, Bello Matawalle wanda ya yi takara a jam'iyyar APC shi ya kalubanci hukuncin karamar kotun a baya.
Kotun ta kuma yi fatali da sakamakon zaben da jam’iyyar APC da kuma hukumar zabe ta INEC su ka bayar a karamar hukumar Maradun.
Martanin jigon jam'iyar APC kan hukuncin
Legit Hausa ta ji ta bakin wani jigon jam'iyyar APC a jihar Gombe, Honarabul Muhammad Abubakar Auwal Akko.
Akko ya ce wannan hukunci abin a yaba ne inda ya ce hukuncin ya yi daidai da abin da mutanen Zamfara su ka zaba.
A cewarsa:
"Wannan hukunci na kotun daukaka kara a jihar Zamfara abin a yaba ne, an yi hukunci daidai da abin da mutane suka zaba.
"Bangaren shari'a ce kadai ta rage wanda talaka ya ke da sauran kwarin gwiwa a kanta.
"Mu na fatan kotun koli za ta tabbatar da wannan hukunci kamar yadda wannan hukunci ya kasance."
Dauda ya sanya dokar ta baci a harkar ilimi
Kun ji cewa, Gwamna Dauda Lawal Dare ya sanya dokar ta baci a bangaren ilimin jihar.
Dauda ya ce hakan ya zama dole ganin yadda gwamnatin baya ta kashe bangaren har kwano.
Asali: Legit.ng