Kotun Daukaka Kara Ta Tsayar da Ranar Juma’a Don Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Kano
- Kotun daukaka mai zamanta a Abuja, ta sanya ranar Juma'a a matsayin ranar yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Kano
- Gwamnan jihar, Abba Kabir, ya daukaka kara kan hukunacin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke, na korarshi daga kujerar
- Kotun kararrakin zaben, a hukuncinta, ta ayyana Nasir Gawuna na jam'iyyar AP matsayin halastacce kuma zababben gwamnnan jihar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta sanya ranar Juma’a domin yanke hukunci kan karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shigar domin kalubalantar tsige shi da kotun sauraron kararrakin zabe ta yi a Kano.
A ranar 20 ga Satumba, 2023, kwamitin wasu alkalai guda uku karkashin jagorancin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay, suka soke nasarar Yusuf.
Kwamitin ya ce akwai kuri'u 165,663 da ba su halatta a sanya su a lissafi ba, sakamakon babu sa hannu ko sitamfin hukumar zabe a jikin su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga nan sai aka rage kuri’un gwamnan zuwa 853,939, yayin da na Nasir Ganuwa, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ke da kuri'u 890,705.
Sai dai, Yusuf ya ki amincewa da hukuncin kotun, wanda ya bayyana a matsayin "tsantsar rashin adalci", inda ya garzaya kotun daukaka kara don kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben.
Lauyan PDP ya kalubalanci hukuncin kotun kararrakin zabe
A kotun, Wole Olanipekun, SAN, lauya mai kare Yusuf, ya bukaci kotun daukaka karar ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron zabe da ya tsige gwamna Yusuf daga kujerar gwamnan jihar Kano, kamar yadda ta The Cable ta ruwaito.
Da yake martani kan hujjar da kotun ta kalla ta yanke hukuncin, babban lauyan ya ce wannan shi ne karo na farko a tarihi da kotu, sauraron kararrakin zabe za ta soke zaben da aka yi kan rashin sanya hannu a jikin kuri'u.
Ya ce kotun kararrakin zaben ta yi kuskure, sannan wannan ne karo na farko da wata jam’iyyar siyasa za ta shigar da kara ba tare da hada wa da dan takararta ba, kuma har kotu ta bayyana dan takarar matsayin wanda ya lashe zaben.
Lauyan APC ya kare hukuncin kotun kararrakin zabe
Sai dai lauyan APC, Akin Olujimi SAN, ya yi masa martani yana mai cewa kotun daukaka kara ta bayyana karara cewa rashin sanya hannu kan takardun kuri’u za a kalle shi a matsayin magudin zabe.
Ya kara da cewa dokokin INEC sun bayyana abin da shugabannin za su yi a lokacin kada kuri’a, inda ya ce dole ne a sanya hannu a jikin takardar kada kur'a tare da kwanan wata.
Kotun daukaka karar ta jingine hukunci a ranar, inda ta ce za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci ga wadanda abin ya shafa.
A ranar Alhamis ne kotun daukaka karar ta bayyana cewa za ta yanke hukunci a ranar Juma'a, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng