Atiku Na Cikin Jalala, Jam'iyyar Adawa Daya Ta Yi Martani Kan Hadin Kan Jam'iyyu a Kasar
- Atiku Abubakar na cikin matsala bayan jam'iyyar LP ta yi martani kan hadin kan jam'iyyun adawa
- LP ta bayyana cewa babu wata hadaka da ta yi da wasu jam'iyyu a kasar bayan neman hadin kai da Atiku ya yi
- Sakataren yada labaran jam'iyyar, Obiorah Ifoh shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Alhamis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jam'iyyar LP ta yi martani kan jita-jitar cewa ta yi hadaka da sauran jam'iyyun adawa.
Sakataren yada labarai na jam'iyyar, Obiorah Ifoh shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Alhamis 16 ga watan Nuwamba.
Mene Atiku ya nema a wurin jam'iyyun adawa?
Obiorah ya ce wannan kirkirarren labari ne da aka hada don bata wa jam'iyyar suna a idon 'yan Najeriya, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne yayin da aka yada jita-jitar cewa jam'iyyar ta amince da kiran Atiku Abubakar na hada kai a kasar.
Atiku ya kirayi hadin kan jam'iyyun adawa a kasar don kwato mulki daga jam'iyyar APC mai mulki, cewar Leadership.
Mene jam'iyyar LP ke cewa ga Atiku?
A cikin sanarwar Obiorah ya ce:
"Ina kira ga mutane da su yi watsi da wannan labarin kanzon kurege da ke yawo cewa LP ta hada kai da sauran jam'iyyu.
"Wannan labarin an kirkire shi ne don bata wa jam'iyyar LP suna a idon duniya.
"Wannan kira ne Atiku ya yi kuma ko wane dan Najeriya ya na da damar ba da gudunmawa wurin inganta dimukradiyya."
Obiorah ya ce don haka babu inda jam'iyyar LP ta yi martani kan wannan kudiri na hadin kan jam'iyyun adawa.
Atiku ya nemi hadin kan jam'iyyun adawa
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nemi hadin kan jam'iyyun adawa a kasar.
Atiku ya nemi wannan hadin kan ne don ganin an tunbuke jam'iyyar APC mai mulki da ta mayar da kasar tsarin mulkin jam'iyya daya.
Wannan kira na zuwa ne bayan shan kaye da jam'iyyun adawa suka yi a hannun APC a zaben da aka gudanar.
Asali: Legit.ng