2027: Peter Obi Sun Shirya Hada Kai da PDP, NNPP Ta Ba Atiku Abubakar Sharadi Mai Wahala

2027: Peter Obi Sun Shirya Hada Kai da PDP, NNPP Ta Ba Atiku Abubakar Sharadi Mai Wahala

  • LP ta maida martani ga Atiku Abubakar wanda yake so jam’iyyun adawa su hada-kai domin su karbi mulki daga hannun APC
  • Kakakin LP na kasa ya yi maraba da wannan shawara da ‘dan takaran PDP ya kawo, amma za a fuskanci matsala daga NNPP
  • Jam’iyyar hamayya ta NNPP ta ce idan za a dunkule, dole ne Atiku ya hakura da burinsa, ya sallamawa Dr. Rabiu Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Jam’iyyar hamayya ta LP ta yi na’am da shawarar da Atiku Abubakar ya kawo na cewa akwai bukatar jam’iyyun adawa su hada-kai.

A ranar Alhamis, Punch ta kawo rahoto cewa LP ta yi maraba da kiran da ‘dan takaran PDP ya yi, jam’iyyar ta ce wannan abin a duba ne.

Kara karanta wannan

Abubuwa Za Su Sukurkucewa Dino Melaye, APC Ta Kawo Hujjar Daure ‘Dan Takaran PDP

Atiku Abubakar
'Dan takaran PDP wajen zaben Kogi Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

APC ba ta tsoron PDP, LP da NNPP

Amma jam’iyyar NNPP ta ce za ta goyi bayan hadin-kan ne da idan Atiku Abubakar zai bi bayan ‘dan takaranta watau Rabiu Musa Kwanwaso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPP ta na ganin Rabiu Musa Kwanwaso ne wanda zai iya karbe mulki a hannun APC a 2027, jam’iyya mai-ci ta ce taron dangi bai ba ta tsoro.

LP za ta iya hada-kai da Atiku da PDP

Da aka zanta da Sakataren yada labaran LP na rikon kwarya, Obiora Ifoh, ya ce ya kamata duk ‘dan Najeriya ya duba maganar da Atiku ya yi.

Cif Obiora Ifoh ya nuna jam’iyyarsu ta LP a shirye ta ke a hada-kai da nufin a ceci tsarin damukaradiyya har kuma a samu mulkin Najeriya.

...wajibin Atiku ya bi Kwankwaso - NNPP

Amma NNPP ta na ganin Atiku ya na ihu ne bayan hari domin aikin gama ya gama tun da PDP da LP su ka sha kashi a zaben 2023 da kotu.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya fara kiran Obi, Kwankwaso da sauran jam’iyyun adawa su hada-kai

Yakubu Shendam wanda shi ne sakataren yada labarai na kasa a NNPP, ya ce duk wata hadaka da za ayi, Rabiu Kwankwaso za a ba takara.

Idan dai ba Kwankwaso zai samu tikiti ba, jam’iyyar NNPP ba za ta hada-kai da kowa ba.

2027: Jam'iyyar PDP ta makara?

"Ihu bayan hari ne. idan har za ayi wani hadin-kai nan gaba, Za mu gwabza mu kadai ne domin mu na da gwarzon da zai iya karbe Najeriya.
Mun yi imani akwai bukatar a nemi goyon bayan mutane daga ko ina domin zabe, mun yarda Kwankwaso shi kadai zai iya kai labari a 2027.”

Atiku, Kwankwaso da Obi za su hadu?

A makon nan aka rahoto Atiku Abubakar ya na fadawa shugabannin IPAC cewa ya kamata ‘yan adawa su dunkule, su yaki gwamnati mai-ci.

Tsohon mataimakin shugaban kasar a matsayinsa na jagoran adawa a Najeriya ya na ganin idan aka yi sake, APC za ta murkushe adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng