Filato: Gabannin Hukuncin Kotun Daukaka Kara, Malamin Addini Ya Yi Gagarumin Gargadi Ga Gwamna

Filato: Gabannin Hukuncin Kotun Daukaka Kara, Malamin Addini Ya Yi Gagarumin Gargadi Ga Gwamna

  • Primate Elijah Ayodele ya ce jam'iyyar APC a jihar Filato ta jajirce don tsige Gwamna Caleb Mutfwang
  • Furucin malamin addinin na zuwa ne yayin da kotun daukaka kara ke gab da yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Filato kafin karshen makon nan
  • Tuni kotun daukaka karar ta tanadi hukunci a karar da dan takarar gwamnan APC, Nentawe Yilwatda Goshwe, ya daukaka yana kalualantar nasarar zaben Mufwang

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jos, jihar Plateau - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele ya bayyana a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, cewa akwai sarkakiya a shari'ar zaben gwamnan jihar Filato.

Primate Ayodele ya ce gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang "yana bukatar addu'a" idan yana fatan hana kotun daukaka kara ta tsige shi daga kujerarsa.

Kara karanta wannan

Kano: Primate Ayodele ya aika sakon gargadi ga Abba Gida-Gida yayin da kotu ke shirin yanke hukunci

Primate Ayodele ya yi hasashen shari'ar zaben gwamnan Filato a kotun daukaka kara
Filato: Gabannin Hukuncin Kotun Daukaka Kara, Malamin Addini Ya Aika Gagarumin Gargadi Ga Gwamna Hoto: Nentawe Yilwatda Goshwe, Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Filato: Shari'ar zaben gwamna na da matukar zafi

Malamin addinin ya bukaci Mutfwang da ya nemi "taimakon Allah", yana mai cewa damar da gwamnan ke da shi na kaucewa tsige shi bai da karfi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Primate Ayodele, jam'iyyar APC ta jajirce don tsige gwamnan na Filato mai ci kuma jigon PDP daga kan kujerarsa.

Primate Ayodele ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya).

"Shari'ar aben gwamnan Filato abu ne mai girma fa. Har yanzu gwamnan na bukatar addu'a, ya nemi taimakon Allah, don kada ya fuskanci aradu. Yana iya shan kan wannan idan ya nemi taimakon Allah. Amma damarsa na tsallakewa bata da karfi. Sai dai kuma, Allah na iya taimakonsa.
"Yanzu dai ya dage da addu'a sosai, idan ba haka ba, APC ta kammala shiri tsaf don tsige shi. Ya zama dole ya yi aiki sosai don kada haka ya faru."

Kara karanta wannan

Yanzu yanzu: Kotun daukaka kara na shirin yanke hukunci a karar da ke neman tsige gwamnan APC

Primate Ayodele ya gargadi Abba gida-gida

A wani labari makamancin wannan, Legit Hausa ta kawo a baya cewa babban malamin addini a Najeriya, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya ce Gwamna Abba Yusuf, na bukatar taimakon Allah kan karar zabe da ya daukaka.

Ku tuna cewa a farkon watan Nuwamba, kotun daukaka kara a Abuja, ta tanadi hukunci a karar da Gwamna Yusuf ya daukaka don kalubalantar tsige shi da kotun zaben gwamna ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng