Kano: Primate Ayodele Ya Aika Sakon Gargadi Ga Abba Gida-Gida Yayin da Kotu Ke Shirin Yanke Hukunci
- Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta tsige Gwamna Abba Yusuf a watan Satumba
- Gwamna Yusuf ya kasance jigon jam'iyyar NNPP kuma dan gidan tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso
- Kotun zaben ta ayyana dan takarar APC, Nasiru Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaben, amma yanzu haka batun na a kotun daukaka kara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Kano, jihar Kano - Babban malamin addini a Najeriya, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya ce Gwamna Abba Yusuf, na bukatar taimakon Allah kan karar zabe da ya daukaka.
Ku tuna cewa a farkon watan Nuwamba, kotun daukaka kara a Abuja, ta tanadi hukunci a karar da Gwamna Yusuf ya daukaka don kalubalantar tsige shi da kotun zaben gwamna ta yi.
Kada ka yi bacci, Ayodele ga Abba gida-gida
Kotun ta tanadi hukunci a dukka kararrakin NNPP mai mulki da jam'iyyar adawa, APC, har zuwa wata rana da za a sanar da bangarorin da ke cikin karar da aka daukaka.
'Inconclusive': Kotu ta ayyana zaben gwamnan Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba, za a sake zabe
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake martani gabannin zama na gaba, Primate Ayodele ya bayyana cewa Gwamna Yusuf na bukatar goyon bayan Allah domin dage hukuncin kotun zaben.
Malamin ya ce:
“Haka kuma hukuncin Kano ma, NNPP ko ma gwamna mai ci. Sun ture shi, kusan kashi 90 cikin 100 ya rage masa ya yi waje. Amma da taimakon Allah, har yanzu yana iya yin nasara. Amma dai yadda abun yake a yanzu, kamar yana so ya lalata ... ya cire tsarin.
"Don haka kada gwamnan ya yi kasa a gwiwa a kokarinsa, ya zama dole ya hana kansa bacci. Kada ya yi."
"Kano ta APC ce": Ayodele
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa babban malamin addini a Najeriya, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC ce za ta sake samun nasara idan jam'iyyar NNPP ta daukaka kara kan hukuncin tsige Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano.
Ayodele ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba. Legit Hausa ce ta gano bidiyon.
Malamin addinin ya ce idan har alkalan ba su yi magudi ba, APC za ta sake kayar da NNPP.
Asali: Legit.ng