Ododo: Mutum 4 a APC da Su ka Share Mani Hanya Aka Zabe Ni Gwamnan Jihar Kogi

Ododo: Mutum 4 a APC da Su ka Share Mani Hanya Aka Zabe Ni Gwamnan Jihar Kogi

  • Ahmed Usman Ododo ya fitar da jawabi bayan an tabbatar da shi ne ya yi nasara a zaben sabon Gwamnan jihar Kogi
  • ‘Dan takaran na APC ya ce tun da Bola Ahmed Tinubu ya mika masa tutan APC, ya san zai yi galaba a takarar da za ayi
  • Ododo ya jinjinawa Gwamna Yahaya Bello da wasu manyan jam’iyya, ta sanadiyyarsu ne zai yi mulki a Kogi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kogo - A jawabin da ya fitar a makon nan, Ahmed Usman Ododo ya fadi wadanda su ka taimaka masa cin zaben gwamnan jihar Kogi.

‘Dan takaran na APC kuma zababben Gwamna ya alakanta nasararsa da Mai gram Bola Ahmed Tinubu, Daily Trust ta fitar da rahoton.

OfficialAPCNg
Zababben Gwamnan Kogi, Ahmed Usman Ododo Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Tinubu da Kashim sun taimaki Ododo

Alhaji Ahmed Usman Ododo yake cewa tun da shugaban kasa ya damka masa tutan jam’iyyar APC, ya san cewa shi ne zai yi galaba.

Kara karanta wannan

Fani-Kayode ya caccaki Dino Melaye kan kayen da ya sha a zaben Kogi: “Allah Sarki Dino, ya zo na 3”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zababben gwamnan jihar Kogi ya kara da cewa jawabin da Kashim Shettima ya gabatar wajen bude yakin neman zabe ya karfafi APC.

Ododo ya godewa gudumuwar da ya samu daga masu ruwa da tsaka dabam-dabam a APC, daga ciki har da Abdullahi Umar Ganduje.

Jawabin Ahmed Usman Ododo

"Godiya ta musamman ga shugabanmu na kasa kuma shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, GCFR da ya share mana fage, ya samar da kafar yin zabe ga kowane ‘dan takara cikin kwanciyar hankali da adalci.
Daga lokacin da ya mika mani tutan, na san zan yi nasara. Ya kasance kafar samun nasara ga miliyoyin da ke kasarmu.
Kuma za mu yi aiki tare da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancinsa kamar yadda jagora na, Alhaji Yahaya Bello yake yi domin kawowa jiharmu cigaba.
Mataimakin shugaban kasa, Mai girma Kashim Shettima, GCON, jawabinka wajen buda kamfe ya zama mana kwarin gwiwa wajen cin zabe."

Kara karanta wannan

"Allah ya ba ku ikon sauke nauyi", Tinubu ya taya Diri, Ododo, Uzodimma murna

- Ahmed Usman Ododo

A jawabin nan sa, rahoton ya ce ‘dan siyasar ya jinjinawa shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ya taimaka masu.

Gwamnan mai jiran gado ya yabawa Yahaya Bello wanda ya ce zai cigaba da zama abin koyi kamar yadda Sahara Repoters ta kawo rahoto.

Ga mutanen jihar ta Kogi kuwa, Ododo ya yi alkawarin zai yi masu aiki da kyau idan ya karbi ragamar mulki daga hannun mai gidan na sa.

Tallafin Remi Tinubu ga iyalan sojoji

A karkashin tsarin inganta rayuwar marasa galihu, labari ya zo cewa uwargidar shugaba kasa, Sanata Remi Tinubu ta ba zaurawa 1709 jarin kudi

Kowace bazawara wanda mijinta ya mutu wajen kare al’umma ta tashi da tallafin N250, 000 ta yadda za su iya dawainiya da marayun hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng