Kotun Daukaka Kara Ta Shirya Raba Gardama Kan Shari'ar Zaben Gwamnan APC a Jihar Arewa
- Yayin da ake ci gaba da shari'ar zaben gwamna a jihar Sokoto, kotun daukaka ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben a yau Talata
- A baya kotun zabe ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar
- Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Sa'idu Umar saboda rashin gamsassun hujjoji
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Kotun daukaka kara ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan da Sa'idu Umar na jam'iyyar PDP ya shigar a jihar Sokoto.
Umar da jam'iyyar PDP sun kalubalanci hukuncin karamar kotun a watan Satumba da ta bai wa Gwamna Aliyu na APC nasara.
Mene kotun ta ce kan hukuncin a karar?
Alkalan kotun wanda Mai Shari'a, Joseph Ekanem ya jagoranta ya bayyana cewa za su sanar da ranar yanke hukunci, The Nation ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkalan sun saurari korafe-korafe daga ko wane bangane a yau Talata 14 ga watan Nuwamba a Abuja.
Lauyan wanda ya shigar da kara, Sunday Ameh ya bayyana cewa akwai kura-kurai a hukuncin karamar kotun da ta yanke a watan Satumba.
Wane roko lauyan ya yi kan shari'ar?
Ameh ya yi korafi kan yadda kotun ta yi watsi da shaidun wanda ya shigar da kara yayin da ke hukuncin a Abuja, Daily Post ta tattaro.
Ya roki kotun daukaka karar da ta yi watsi da hukuncin karamar kotun wurin tabbatar da wanda ya shigar da kara a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.
Kotu ta adana shari'ar zaben gwamna a Plateau
A wani labarin, kotun daukaka kara ta tanadi hukunci a karar da ake yi na korafe-korafen zaben gwamna a jihar Plateau.
Kotun sauraran kararrakin zabe a baya ta yi hukunci inda ta tabbatar da Caleb Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.
Har ila yau, kotun ta yi fatali da karar dan takarar jam'iyyar PDP, Nentawe Goshwe saboda rashin gamsassun hujjoji da za su rusa zaben gwamnan.
Asali: Legit.ng