Gwamnan APC Ya Gano Gaskiya, Ya Umarci Wasu Ma'aikatan Gwamnati Su Yi Murabus a Jihar Arewa
- Gwamna Ahmed Aliyu ya umarci sakatarorin kananan hukumomin jihar Sakkwato su aje aikin Gwamnati
- Ya ce tunda ta tabbata muƙaman da aka naɗa su na siyasa ne, ya zama wajibi su bi doka duk wanda ke aikin Gwamnati ya aje shi
- Ya kuma umarci shugabannin kananan hukumomi da su maida hankali kan magance matsalar tsaro a yankunansu
Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya umarci ma’aikatan gwamnati da aka nada a matsayin sakatarorin kananan hukumomi su aje aikin gwmanati.
Gwamnan na jam'iyyar APC ya umarci su gaggauta yin murabus ne saboda muƙaman da aka naɗa su na siyasa ne, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Gwamnan ya ba da umarnin ne jim kadan bayan ganawarsa da shugabannin kananan hukumomi da sakatarorin su na fadin jihar.
Ya ce duk wani cece-kucen da ke tattare da mukamin sakatarorin kananan hukumomi ya kare saboda doka ta ayyana su cikin masu rike da mukaman siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A rahoton Tribune Online, Gwamnan ya ce:
“Yanzu ta tabbata cewa kuna rike ne da ofisoshin siyasa, don haka duk wanda ya san shi ma’aikacin gwamnati ne ya tabbatar ya aje aikin. Mun yi imani da doka ba zamu bar ko waye ya karya doka ba."
Gwamna Aliyu ya gargaɗi shugabannin kananan hukumomi
Gwamna Aliyu ya umarci shugabannin kananan hukumomin su tabbata suna kiran taron tsaro a kai a kai da masu ruwa da tsaki a fannin domin nazari kan ayyukan ta'addanci a yankunansu.
"Tabbatar da tsaro ga al'ummar mu ba alhaki ne da ya rataya a wuyan Gwamnati kaɗai ba, ya rataya a wuyan kowa," in ji shi.
Ya kuma gargaɗi masu jagorantar gwamnatocin kananan hukumomin jihar Sakkwato da su jawo kowa a jiki kan sha'anin tsaro domin cimma nasara mai ɗorewa.
Gwamna Aliyu ya kara da cewa su kiyaye tare da kai rahoton duk abin da ba su aminta da shi ba ga hukumomin da ya dace domin daukar mataki.
Sanata Melaye ya ba INEC wa'adi
A wani rahoton kuma Sanata Dino Melaye na PDP ya ce INEC na da wa'adin kwana bakwai ta duba ƙorafin da ya kai mata kan zaɓen Gwamnan jihar Kogi
Ɗan takarar Gwamna a inuwar PDP ya ce tuni ya miƙa kokensa ga INEC kan abubuwan da ya hango sun faru a lokacin zaɓe.
Asali: Legit.ng