Kotu Za Ta Yanke Hukuncin Shari’ar Abba da Gawuna, ‘Yan Sanda Sun Tsaurara Tsaro a Kano
- Ana sa ran kotun daukaka kara tayi hukunci tsakanin Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna a kan zaben Kano
- A dalilin haka sanarwa ta fito cewa Rundunar ‘yan sanda ta baza jami’an tsaro zuwa wasu muhimman wurare a jihar
- Kwamishinan ‘Yan Sandan na Kano ya ce an dauki matakan ne saboda a tabbatar da kariya ga rayuwa da dukiyoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Rundunar ‘yan sanda na jihar Kano ta kara tsaro yayin da ake shirin yin hukunci a shari’ar zaben Gwamna a garin Abuja.
A ranar Litinin, Leadership ta ce rundunar ‘yan sandan reshen Kano ta shaida cewa an baza dakaru zuwa wurare na musamman.
Zaben Gwamna: 'Yan Sanda sun fitar da sanarwa
‘Yan sanda sun yi hakan ne saboda tabbatar da kare dukiya da rayukan al’ummar jihar Kano daga rikicin siyasa da zai iya tashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ‘yan sanda ya sanar da matakan da aka dauka a jawabin da ya fitar ta bakin kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa.
CP Muhammad Usaini Gumel ya ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ba za su bari miyagu su kawo hatsaniyar siyasa a jihar Kano ba.
Matakan da aka dauka a Jihar Kano
“‘Yan sanda da sauran jami’an tsaro suna tabbatar da tsaron mutanen Kano kafin, zuwa lokaci da kua bayan an zartar da hukuncin zabe,”
Ana sa ran mutanen kirkin Kano za su taka rawar ganinsu wajen hana barkewar rikici.
A dalilin haka ana sanar da wadannan gargadi:
Ba za a amince da ta tara mutane da manufar siyasa a karkashin kowane irin yanayi ba.
A guji cincirindo da ke nuna shirin tattaki dauke ta tarzoma, zanga-zanga ko nuna farin ciki.
A guji kalamai marasa linzami daga bakin ‘yan siyasa da za su iya jawo karin tashin hankali ko barazana ga tsaro ko martabar shari’a."
- Kwamishinan 'yan sandan Kano
Shari'ar zaben Gwamnan Kano
Kotun daukaka kara ta saurari shari’ar zaben gwamnan jihar Kano, kuma an ji labari an tanadi lokacin yin hukunci, sai dai ba a sanar ba tukuna.
Ana shari’a ne tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ‘dan takaran APC, Nasiru Yusuf Gawuna wanda kotun korafin zabe ta ba gaskiya a baya.
Asali: Legit.ng