Dalilai 6 da Su Ka yi Sanadin Galabar Ahmed Ododo da APC a Zaben Gwamnan Kogi
- Ahmed Usman Ododo ya lashe zaben sabon gwamna a jihar Kogi, ya doke jam’iyyun hamayya na SDP, PDP da ADC
- Nasarar APC bai zo da mamaki sosai ba idan aka duba cewa Jam’iyyar ce ta ke kan mulki kuma kan ‘yan adawa ya rabu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Kogi - Hukumar INEC ta tabbatar da Ahmed Usman Ododo a matsayin wanda ya lashe zaben sabon gwamna da aka yi a jihar Kogi.
A wannan rahoto, Legit ta duba abubuwan da su ka taimaka wajen nasarar jam’iyyar APC.
1. Karfin mulkin APC a kasa da Kogi
Kamar yadda mu ka saba fada, a siyasar Najeriya jam’iyya mai-ci da shugaban da yake kan mulki yana da karfi idan ana maganar zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai girma Gwamna Yahaya Bello mai shirin barin gadon mulki ya taka kusan dukkan rawar gani domin Ahmed Usman Ododo ya ci zabe.
2. Siyasar kabilancin jihar Kogi
A baya mun rahoto cewa kabilanci zai iya yin tasiri a zaben Kogi, hakan ta faru idan aka duba kuri’un Kogi ta tsakiya da kuma Kogi ta gabas.
Ebira sun marawa Ododo bayan kamar yadda ‘yan kabilar Igala sun zabi Murtala Ajaka, sai dai SDP ba ta samu kuri’u a sauran yankuna ba.
3. KogiDecides: Jami’an tsaro da INEC
‘Yan adawa da sauran kungiyoyi masu sa ido suna zargin an yi magudi ta hanyar aringizon kuri’u musamman a yankin tsakiyar jihar Kogi a zaben.
APC ta samu kuri’u masu ‘dan karen yawa a irinsu Okene, Adavi da Ajaokuta wanda wasu su ke zargin hukumar INEC da jami’an tsaro sun yi sake.
4. SDP, PDP ko ADC?
Jam’iyyar adawa ta rabu gida uku a zaben wanda hakan ya ba APC damar yin galaba cikin sauki. An raba kuri’u tsakanin SDP, PDP da kuma ADC.
‘Yan takaran jam’iyyun PDP da ADC sun hana Murtala Ajaka na SDP ya iya samun kuri’un da zai karbe mulki daga hannun APC a yammacin Kogi.
5. Rigingimun PDP a reshen Kogi
Bayan yadda ‘yan takara su ka jawo rabuwar kai a zaben, Legit ta na ganin barakar PDP ta fito fili a zaben, wasu sun ki goyon bayan Dino Melaye.
An yi ta guna-guni da Dino Melaye ya doke irinsu Musa Wada wajen samu tikitin jam’iyyar PDP. Watakila wannan ya ba APC kuri’u a yammacin jihar.
6. Kudi
Siyasar Najeriya tana tafiya ne da kudi tun daga wajen samun takara, yakin neman zabe, shirye-shirye da kuma kudin da ake batarwa a lokacin zaben.
APC a matsayin jam’iyyar da ke da gwamnati kuma mai mulki ba za ta rasa kudin batarwa ba, musamman lura da adadin kujerun ta a majalisu.
APC ta kunyata Dino Melaye a Kogi
PDP ta fadi a karamar hukumar Kabba Bunu da kuma Ijumu, inda ake ganin Sanata Dino Melaye zai iya kai labari domin nan ne kauyensa.
Jam’iyyar APC mai-ci ta sha gaban Dino Melaye da kuri’u kusan 4000 a Kabba Bunu a zaben Gwamna kamar yadda ku ka samu rahoto tun jiya.
Asali: Legit.ng