Buhari Ya Aike da Saƙo Mai Muhimmanci Kan Sakamakon Zaɓen Gwamnan Jihohin Imo da Ƙogi
- An gudanar da zaɓen gwamnan jihar Kogi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023 domin zaɓen sabon gwamna
- Hakazalika a wannan ranar an gudanar da irin wannan zaɓen a jihar Imo da jihar Bayelsa da ke yankin Niger Delta
- A jihohin Kogi da Imo, jam’iyyar APC mai mulki ta doke jam'iyyun adawa da suka fafata a zaɓen gwamnan na ranar Asabar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Lokoja, jihar Kogi - Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, ya taya jam’iyyar All Progressives Congress (APC) murnar lashe zaben gwamna a jihohin Imo da Kogi.
Buhari, a cikin wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawunsa ya rabawa manema labarai, ya godewa al’ummar jihohin biyu "saboda sake jaddada amincewarsu da babbar jam’iyyar siyasar ƙasar nan."
"Fatan alheri", Buhari ya gaya wa Ododo, Uzodimma
Tsohon shugaban ya bayyana godiyarsa musamman ga shugabannin jam’iyyar APC da “ma'aikata” waɗanda ya ce sun yi namijin ƙoƙari wajen ganin samun nasarar Hope Uzodimma a karo na biyu a jihar Imo, da kuma Ahmed Usman Ododo a matsayin gwamnan jihar Kogi mai jiran gado.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina yi musu fatan alheri a wa'adin mulkinsu." A cewarsa.
Ganduje ya ta ya Uzodinma da Ododo murna
Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya taya Gwamna Hope Uzodinma murnar nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023.
Ganduje ya kuma taya zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo, murnar lashe zaɓen gwamnan jihar da ya yi.
Uzodinma Ya Fadi Dalilin Kayar da Ƴan Adawa
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Imo a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Hope Uzodinma, ta bayyana dalilin da ya sanya ƴan adawa suka sha kashi a zaɓen gwamnan jihar.
Gwamnatin ta bayyana cewa abokan takarar Gwamna Uzodinma na jam'iyyun PDP da LP, ba su shirya ba domin jam'iyyun su fama su ke yi da rikicin cikin gida.
Asali: Legit.ng