Ganduje Ya Fayyace Babban Abin da Ya Haifar da Nasarar APC a Zaben Kogi da Imo

Ganduje Ya Fayyace Babban Abin da Ya Haifar da Nasarar APC a Zaben Kogi da Imo

  • Abdullahi Umar Ganduje ya ji dadin yadda jam’iyyar APC ta lashe zaben Gwamnonin da aka yi a jihohin Imo da Kogi
  • Shugaban jam’iyyar APC ya ce mutanen jihohin nan sun ji dadin mulkinsu, saboda haka aka nemi su zarce kan karagar mulki
  • Dr. Ganduje ya ce Hope Uzodinma zai cika alkawuransa, kuma Ahmed Ododo zai yi koyi da ayyukan Yahaya Bello a jihar Kogi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya taya Hope Uzodimma murnar lashe zaben Gwamnan Imo.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fitar da jawabi na musamman a ranar Lahadi, ya na farin cikin murnar da APC ta samu a Imo da Kogi.

Kara karanta wannan

Farfesa Yakubu Yana Fuskantar Barazanar Zuwa Gidan Yari a Kujerar Shugaban INEC

Abdullahi Ganduje
Shugabannin APC kafin zaben Kogi da Imo Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Dr. Ganduje ya yi farin cikin lashe zabe

Jawabin ya fito ne ta bakin Babban sakataren yada labaran shugaban na APC, Edwin Olofu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Umar Ganduje ya kuma nuna farin cikinsa a kan yadda mutanen jihar Kogi su ka zabi Alhaji Usman Ododo a takarar Gwamna.

Meya jawo aka zabi APC a Kogi, Imo?

Shugaban jam’iyyar mai mulki yake cewa galabar da su ka samu a jihohin nan biyu ya nuna al’umma sun gamsu da salon shugabancin APC.

Dr. Ganduje ya na ganin rikon da Hope Uzodimma da Gwamna Yahaya Bello mai barin-gado su ka yi wa jama’a ya sa aka sake zaben APC.

'Yan adawan Kogi da Imo za su hakura?

Punch ta ce tsohon gwamnan na jihar Kano ya yi kira ga ‘yan adawa da su ka sha kashi wajen takarar gwamnan da su rungumi kaddara.

Kara karanta wannan

Zabe ya kammala a Kogi, INEC ta sanar da wanda ya lashe zabe, ya fi kowa adadin kuri'u

Tuni aka ji Dino Melaye da Murtala Ajaka sun bukaci a soke zaben da aka gudanar a Kogi.

A jihar Imo, ‘dan takaran jam’iyyar hamayya ta LP ya zargi jami’an tsaro da hada-kai da jam’iyya mai ci domin ganin Uzodinma ya zarce.

Kogi, Imo: Jawabin Dr. Abdullahi Umar Ganduje

"Abin da ya yi mani dadi game da nasarorin jihohin Kogi da Imo shi ne ‘Yan Najeriya sun yaba da mulki nagari kuma su na son zarcewar kwanciyar hankali da cigaba a jihohinsu.
A matsayin jam’iyya mai son cigaba, za mu cika alkawuranmu na yin ayyukan kwarai."

- Abdullahi Umar Ganduje

Babu labarin PDP a zaben Kogi

An samu rahoton da ya nuna jam'iyyar PDP ta fadi a karamar hukumar Kabba/Bunu, inda ake ganin Sanata Dino Melaye zai iya kai labari a zaben.

Daga shekarar 2007 zuwa 2011, ‘Dan takaran Gwamnan PDP ne ya wakilci yankin a majalisar tarayya sai ga shi ya rasa Kabba da Ijumu ga APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng