Usman Ododo Na APC Ya Lallasa Abokan Hamayarsa a Karamar Hukumarsa Da Tazara Mai Yawa
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Okene, Jihar Kogi - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa, a ranar Lahadi 12 ga watan Nuwamba, ta yi nasara a karamar hukumar Okene na jihar Kogi a zaben gwamna na 2023 a jihar.
A cewar Hukumar Zabe mai Zaman Kanta na Kasa (INEC), Ahmed Ododo na jam'iyyar APC ya kayar da Dino Melaye na Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Murtala Ajaka na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben da aka yi a karamar hukumar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ododo ya samu kuri'u 138,416 inda Melaye ya samu kuri'u 1,463 shi kuma Ajaka ya samu kuri'a 217.
Duba kuri'un a nan kamar yadda The Cable ta wallafa.
Masu zabe da suka yi rajista: 151,243
Masu zabe da aka tantance: 141,898
ADC: 261
APC: 138,416
PDP: 1,463
SDP: 271
Kuri'u masu kyau: 141,404
Lalatattun kuri'u: 134
Jimlar kuri'u da aka kada: 141,538
Asali: Legit.ng