Zaɓen Kogi: Ɗan Takarar da Ke Kan Gaba a Tsakanin Ododo, Melaye da Ajaka a Ƙananan Hukumomi 10

Zaɓen Kogi: Ɗan Takarar da Ke Kan Gaba a Tsakanin Ododo, Melaye da Ajaka a Ƙananan Hukumomi 10

  • Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen gwamnan jihar Kogi ya yi nasara a ƙananan hukumomi 10
  • Alhaji Ahmed Usman Ododo ya shiga gaban abokan hamayyarsa a zaɓen na jam'iyyun SDP, PDP da ADC
  • A sakamakon da hukumar zaɓen ta sanar na ƙananan hukumomi 10, Ododo ya samu ƙuri'u 207,293

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Alhaji Ahmed Usman Ododo ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yana kan gaba a tsakanin abokan hamayyarsa na jam'iyyun PDP, Social Democratic Party (SDP) da African Democratic Congress (ADC).

A sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 10 na jihar kawo yanzu da hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar, ɗan takarar jam'iyyar APC ya na gaban Murtala Ajaka da Dino Melaye da kuma Leke Abejide na jam’iyyun SDP, PDP da ADC.

Kara karanta wannan

Yanzu: Usman Ododo na APC ya lallasa abokan hamayarsa a karamar hukumarsa da tazara mai yawa

Ododo na kan gaba a zaɓen Kogi
Ahmed Usman yana kan gaba bayyana sakamakon ƙananan hukumomi 10 Hoto: Usman Ododo, Dino Melaye, Murtala Ajaka
Asali: Facebook

A wani sako da jaridar TheCable ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce Ododo ne kan gaba a cikin ƙananan hukumomi 10 da ƙuri'u 207,293, yayin da Ajaka ya samu ƙuri’u 59,807 kawo yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya zuwa yanzu Dino Melaye na jam’iyyar PDP ya samu ƙuri'u 21,447, sannan Abejide na jam’iyyar ADC ya samu ƙuri'u 16,632 a ƙananan hukumomi 10 da INEC ta bayyana sakamakonsu a hukumance.

SDP ta lallasa PDP, APC a ƙananan hukumomi 5

Muritala Ajaka, dan takarar jam'iyyar SDP a zaben gwamnan jihar Kogi da aka yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, ya yi gagarumin nasara a kananan hukumomi biyar (5).

Koda dai hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fara tattara sakamakon karshe a jihar, amma dai hukumar bata riga ta sanar da wanda ya lashe zaben ba a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

SDP ta lallasa APC da PDP a kananan hukumomi 5 yayin da ake tattara sakamakon zaben gwamnan Kogi

Ajaka Ya Nemi a Soke Zaɓen Kogi

A wani labarin kuma, ɗan takarar gwamnan jihar Kogi, Alhaji Muritala Ajaka, a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar SDP ya nemi a soke zaɓen gwamnan jihar Kogi.

Ajaka ya buƙaci hukumar zaɓe ta INEC da ta soke zaɓen gwamnan da aka gudanar a yankin Kogi ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng