'Dan Takaran Yahaya Bello a APC Ya Doke PDP a Karamar Hukumar Dino Melaye
- Sanata Dino Melaye ya rasa karamar hukumar Kabba Bunu, inda ake ganin zai iya kai labari a zaben bana
- Daga shekarar 2007 zuwa 2011, ‘Dan takaran na PDP ne ya wakilci mutanen yankin a majalisar tarayya
- Jam’iyyar APC mai-ci ta sha gaban Dino Melaye da kuri’u kusan 4000 a Kabba Bunu a zaben Gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kogi - Jam’iyyar PDP ba ta iya lashe kuri’un Karamar hukumar Kabba Bunu a zaben sabon Gwamnan da ake yi a jihar Kogi ba.
Sanata Dino Melaye da yake takara a PDP mutumin garin Ijumu ne wanda yake kusa da Kabba Bunu inda sakamako ya bayyana.
Kogi: Dino Melaye ya fadi a Kabba Bunu da Ijumu
Abin da zai bada mamaki shi ne Melaye ya taba wakiltar mutanen mazabar Kabba Bunu da Ijumu a majalisar wakilan taayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan takaran gwamnan na PDP a zaben bana ya yi shekaru hudu a kujerar tsakanin 2007 da 2011, a karkashin jam’iyyar PDP.
Bayan nan ya zama Sanata na daukacin yammacin jihar Kogi daga 2015 zuwa 2019.
A karamar hukumar Ijumu, haka labarin yake domin APC ta ci kuri’u 10,524, sai PDP ta samu 6,909 yayin da SDP ta tashi da kuri’u 356.
Ododo zai doke Dino da PDP a Kogi
Sakamakon da hukumar INEC ta sanar ya nuna Ahmed Usman Ododo na jam’iyyar APC ya sha gaban Dino Melaye a Kabba Bunu.
‘Dan takaran jam’iyyar ADC a zaben na Kogi wanda ‘dan majalisa ne, ya zo na uku a karamar hukumar da kuri’u sama da 1500.
Leke Abejide ya na da farin jini musamman a wajen mutanen Yagba da Mopa Moru.
Murtala Ajaka wanda ya fito daga gabashin jihar Kogi ya kare ne da kuri’u 842 kacal, sai LP da NRM su ka kare da kuri’u 7 da 16.
Sakamakon da INEC ta sanar
Ga yadda sakamakon yake:
APC: 12,376
PDP: 8,566
SDP: 942
LP: 07
NRM:16
Wani mataki Dino Melaye zai dauka?
Amma Dino Melaye ya nuna ba za su yarda da sakamakon ba, musamman ganin irin kuri'un da APC ta samu garin Okene kurum.
Sanata Melaye ya ce babu abin da ya dace illa a soke zaben gwamnan da aka shirya.
Zaben Gwamnan Kogi ya dauki zafi
Ana da labari cewa zaben sabon gwamnan jihar Kogi yayi zafi yayin da Gwamnan jihar Imo ya samu gagarumar galaba ya zarce.
Ahmed Usman Ododo da Murtala Yakubu Ajaka suna samun nasara a Kogi ta tsakiya da kuma Kogi ta gabas –yankunan da su ka fito.
Asali: Legit.ng