Kotun Daukaka Kara Ta Shirya Raba Gardama Kan Zaɓen Gwamnan PDP

Kotun Daukaka Kara Ta Shirya Raba Gardama Kan Zaɓen Gwamnan PDP

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta tanadi hukunci kan ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau
  • Ɗan takarar jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda ya shigar da ƙarar a gaban kotun saboda rashin gamsuwa da hukuncin kotun zaɓe ta yanke
  • Kotun zaɓe dai ta yi watsi da ƙarar da Nentawe ya shiga yana ƙalubalantar nasarar Mutfwang a zaɓen gwamnan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta tanadi hukunci a ƙarar da ke ƙalubalantar zaben Gwamna Caleb Mutfwang.

A ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, kotun mai alƙalai uku ta tanadi hukunci a ƙarar bayan ta kammala sauraron bayanai daga lauyoyin ɓangarorin, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar Gwamanan PDP

Kotun ɗaukaka ƙara ta tanadi hukunci kan zaɓen gwamnan Plateau
Gwamna Caleb Mutfwang ya kusa sanin makomarsu Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Nentawe Yilwatda Goshwe ne ya shigar da ƙarar a kan Gwamna Mutfwang da jam'iyyar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nentawe ya ƙalubalanci nasarar Gwamna Mutfwang

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta bayyana Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris da ƙuri’u 525,299, inda ya doke sauran ƴan takara 17 ciki har da Nentawe wanda ya samu ƙuri’u 481,370.

Rashin gamsuwa da zaɓen ya sanya Nentawe ya ƙalubalanci zaben Mutfwang a kotu, yana mai cewa gwamnan bai cancanta ba saboda ba jam'iyyar PDP ta tsayar da shi takara ba.

Hakazalika ya yi zargin cewa ba a gudanar da zaben Mutfwang bisa tsarin dokokin zaɓe ba, kuma bai samu ƙuri'u mafi rinjaye ba a lokacin zaɓen.

Kara karanta wannan

Filato: Bayan tsige 'yan majalisar tarayya, kujerar Gwamnan PDP ta fara tangal-tangal a kotun ɗaukaka kara

Sai dai, kotun zaɓen mai alƙalai uku a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a R. Irele-Ifijeh, a wani hukunci na bai ɗaya ta yi watsi da ƙarar saboda rashin cancanta.

Rashin gamsuwa da hukuncin, ya sanya Nentawe ya ƙara ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun zaɓen, inda ya buƙaci kotun ɗaukaka ƙara da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Zartar da Hukunci Kan Zaɓen Gwamna Mbah

A wani labarin kuma, kotun ɗaukaka ƙara ta zartar da hukunci kan shari'ar da ke.ƙalubalantar nasarar gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, na jam'iyyar PDP.

Kotun mai zamanta a birnin Legas, ta tabbatar da nasarar gwamnan a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18, ga watan Maris 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng