Zaben Imo: An Ba Hammata Iska a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe, Bidiyo Ya Bayyana

Zaben Imo: An Ba Hammata Iska a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe, Bidiyo Ya Bayyana

  • An samu hargitsi a cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Imo, da ke birnin Owerri babban birnin jihar Imo
  • Hargitsin ya fara ne lokacin da wakilin jam'iyyar Labour Party ya nemi kawo cikas saboda rashin yarda da sakamakon zaɓen da a ke tattarawa
  • Hakan ya sanya wakilan sauran jam'iyyu suka yi masa dukan tsiya tare da fitar da shi daga wurinnda ƙarfin tuwo

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Cibiyar tattara bayanan sakamakon zaɓen gwamnan jihar Imo da ke Owerri babban birnin jihar ta shiga ruɗani yayin da aka lakaɗawa wakilin jam'iyyar Labour Party (LP) duka.

Tattara sakamakon zaɓen wanda baturen zaɓen INEC, Farfesa Abayomi Fasina, mataimakin shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Oye, Ekiti ya jagoranta, ya fara ne da karfe 2:40 na daren ranar Lahadi, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Zaɓen Kogi: Hadimin Atiku Ya Caccaki INEC, Ya Bayyana Dalilansa

An lakadawa wakilin LP duka a Imo
Wakilin LP ya sha dukan tsiya a cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamnan Imo Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Tattara sakamakon dai ya fuskanci ƙalubale tun daga lokacin da aka fara, inda wasu wakilan jam'iyyu suka nuna adawar su da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka bugi wakilan Labour Party?

Wakilin jam’iyyar Labour Party (LP) a jihar Imo, Calistus Ihejiagwa, ya sha dukan tsiya sannan aka yi waje da shi daga wajen tattara sakamakon zaɓen, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Wakilin ya cigaba da nuna rashin amincewa da sakamakon da aka tattara daga ƙananan hukumomin, yana mai cewa sakamakon da aka gabatar a gaban cibiyar tattara sakamakon zaɓen ya saba da abin da ke kan manhajar duba sakamakon (IREV).

Ihejiagwa ya sha bayyana cewa yana da takardar koke da zai gabatar a gaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) amma jami’in da ke kula da tattara sakamakom zaɓen, Farfesa Abayomi Fashina ya hana shi, inda ya ce ba huruminsa ba ne karɓar koke.

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke wajen zaɓe a Bayelsa yayin da jami'an INEC suka nemi tsira da ransu, bidiyo ya fito

Sauran wakilan jam'iyyu sun yi wa Ihejiagwa kallon wanda ke son kawo katsalandan wajen tattara sakamakon zaɓen, inda da misalin ƙarfe 5:00 na safe suka yi waje da shi daga cibiyar tattara sakamakon zaɓen, sannan aka cigaba da tattara sakamakon zaɓen.

Hukumar INEC Ta Sha Suka

A wani labarin kuma, Dele Momodu hadimin Atiku Abubakar, ya cacccaki hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) kan dakatar da zaɓe a wasu gundumomi tara na jihar Kogi.

Momodu ya yi nuni da cewa abun kunya ne yadda INEC ba za ta iya gudanar da zaɓe cikin jihohi uku kacal cikin lumana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng