Jami’inmu da Aka Sace Wajen Zaben Gwamnan Bayelsa Ya Samu ‘Yanci Inji Hukumar INEC

Jami’inmu da Aka Sace Wajen Zaben Gwamnan Bayelsa Ya Samu ‘Yanci Inji Hukumar INEC

  • A ranar Juma’a, labari ya shiga ko ina cewa an dauke wani ma’aikacin da INEC ta tura aikin zabe a Jihar Bayelsa
  • Daga baya sanarwa ta fito daga bakin hukumar cewa wannan jami’i ya fito, sai dai ba ayi wani cikakken bayani ba
  • Jami’in da aka dauke ya samu iskar ‘yanci bayan mutane sun kada kuri’u a zaben Gwamnan da aka yi a Bayelsa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bayelsa - Wani ma’aikacin hukumar INEC da aka yi ram da shi a ranar jaji-birin zaben Gwamnan jihar Bayelsa, ya samu ‘yanci.

Wannan jami’i na SPO ya kubuta daga hannun wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shi, Vanguard ta fitar da labarin nan a jiya.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Shakawa Masu Zabe N40, 000 Domin a Saye Kuri’unsu a Zaben Gwamnoni

INEC.
Ma'aikatan INEC a zaben Gwamna Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Ma'aikacin da aka dauke ya fito a Bayelsa

Shugaban sashen wayar da kan masu zabe da kuma harkar yada labarai, Wilfred Ifogah ne ya fitar da wata sanarwa ta musamman.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Wilfred Ifogah ya shaidawa manema labarai cewa jami’in ya shaki iskar ‘yanci.

Hukumar zabe na kasa watau INEC ta godewa duk wani wanda ya bada gudumuwa wajen fito da wannan malamin zabe daga kangi.

Har zuwa yanzu ba a bayyana sunan ma’aikacin ba, INEC dai ta ce yana nan kalau yanzu yayin da ake tattara sakamakon zaben jihar.

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta ce ba a iya samun kakakin ‘yan sandan jihar, Asinim Butswat domin jin ta bakinsa ba.

Baya ga wannan hadari da sace malamin zabe da aka yi a Bayelsa, an samu labarin barkewar rikici a lokacin da ake zaben gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: SDP na bugawa da APC a Kogi, PDP tayi gaba a Bayelsa, APC a Imo

Ya aka yi aka sace jami'in INEC a Bayelsa?

A ranar Juma’a ne Ifogah ya bada sanarwar cewa an yi gaba da wani daga cikin wadanda za su yi aiki a karamar hukumar Sagbama.

A lokacin ne aka fahimci cewa jirgin ruwan da yake dauke da kaya zuwa karamar hukumar Ijaw ta Kudu a jihar ta Bayelsa ya nutse.

An kama 'masu sayen' kuri'u a Imo da Bayelsa

Hukumar EFCC ta ce ta kama mutane 14 dauke da N11m da ake zargin za ayi amfani da su wajen sayen kuri’u a jihohin Bayelsa da Imo.

An samu labari cewa Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya ce sun karbe N9.3m a Bayelsa sai kuma N1.7m a garuruwan Imo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng