Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamanan PDP

Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamanan PDP

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan ƙarar da jam'iyyu biyu suka kalubalanci nasarar Gwamna Eno na Akwa Ibom
  • Yayin yanke hukunci ranar Jumu'a, Kotun ta kori ƙarar AA da AP bisa rashin cancanta, ta amince da hukuncin Kotun zaɓe
  • Bayan haka Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Legas ta tanadi hukunci a karar da APC ta kalubalanci nasarar Gwamnan na PDP

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a jihar Legas ta yi watsi da kararrakin jam'iyyun Action Alliance (AA) da Accord Party (AP) kan zaɓen Gwamnan Akwa Ibom.

Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno.
Kotun Ɗaukaka Kara Ta Kori Karar Jam'iyyu Biyu Kan Nasarar Gwamnan Akwa Ibom Hoto: Umo Eno
Asali: Twitter

Kwamitin alkalai uku ƙarƙashin mai shari'a Tani Hassan ta kori kararrakin biyu waɗanda suka ƙalubalanci nasarar Gwamna Umo Eno na jam'iyyar PDP ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta tanke hukunci kan nasarar ɗan Majalisar Tarayya bayan kotun zaɓe ta tsige shi

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa yayin da take karanto hukuncin, Mai shari'a Tani Hassan ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na warware ƙorafin masu shigar da ƙara kuma na tabbatar da hukuncin da Kotun zaɓe ta yanke. Na kori ƙarar bisa rashin cancanta."

Yadda shari'ar ta kaya a gaban Kotu

Tun da farko, jam'iyyar AA da ɗan takararta na Gwamna, Akpan Udolt, sun yi zargin cewa babu sunan jam'iyyar a takardar kada kuri'a, bisa haka suka roƙi Kotu ta soke zaben.

Amma Gwamna Eno da jam'iyyarsa PDP sun roƙi Kotun da kada ta saurari bayanan jam'iyyar AA.

Mista Paul Usoro (SAN), lauyan jam’iyyar PDP da gwamnan Akwa Ibom, ya yi musun cewa wadanda suka shigar da karar ba su da hurumin kawo ƙara gaban Kotu.

Lauyan ya kafa hujja da tanadin sashi na 133 (1) wanda ke ƙunshe a kundin dokokin zaɓe 2022, kamar yadda jaridar The Angle ta ruwaito.

Kara karanta wannan

To Fa: Ana jajibirin zaɓe, Ɗan takarar Gwamna na jam'iyyar APC ya sha da ƙyar, bayanai sun fito

Ya kuma bayyana cewa sashe na 133(1) na dokar zabe ya bayyana karara cewa masu kara ba su da hurumin ɗaukaka wannan ƙara, don haka ya roƙi a kori karar.

Kotun ɗaukaka ƙara ta kuma tanadi hukunci kan ƙarar da jam'iyyar APC ta ƙalubalanci nasarar Gwamna Eno, ta ce zata sanar da ranar bayyana hukuncin nan gaba.

Gwamna Oborevwori Ya Ziyarci Tsohon Shugaban NUPENG a Asibiti

A wani rahoton kuma Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya ziyarci dattijon ƙasa kuma babban jigon APC da ke jinya a Asibiti.

Ya ɗauki nauyin duk wata hidima da kuɗin kula da lafiyarsa, yana mai cewa ya cancanci haka duba da gudummuwar da ya bada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262