Zaben Kogi: ’Yan Sanda Sun Gargadi ’Yan Arewa Masu Zuwa Kudanci Su Sauya Tunani, Sun Fadi Mafita
- Rundunar 'yan sanda a jihar Kogi ta shawarci masu tafiya zuwa Kudancin Najeriya da su nemo wata hanya
- Kakakin rundunar a jihar, SP Williams Ayah shi ya bayyana haka inda ya ce an hana zirga-zirgar ababawan hawa a jihar
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi a gobe Asabar 11 ga watan Nuwamba
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Yayin da ake shirye-shiryen zaben gwamna a jihar Kogi, 'yan sanda sun shawarci matafiya zuwa Kudancin Najeriya.
Mataimakin Sifetan 'yan sanda a Kogi shi ya ba da wannan shawara inda ya ce ma su zuwa Kudancin kasar su nemi wata hanya daban, cewar Trust Radio
Wane gargadi 'yan sanda su ka yi kan zaben Kogi?
Kakakin rundunar a jihar, SP Williams Ovye Ayah shi ya bayyana haka a yau Juma'a 10 a watan Nuwamba, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayah ya ce ma su zuwa yankin Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas da ke bin hanyar Lokoja zuwa Okene su bi wata hanya.
Ya ce wannan umarni ya biyo bayan hana zirga-zigar ababawan hawa da Mataimakin Sifetan 'Yan Sanda a jihar ya kaddamar kan zabe a jihar.
Wane roko rundunar ta yi ga mutane?
Ya ce za a hana zirga-zirgar ababan hawa daga yau Juma'a 10 ga watan Nuwamba da misalin karfe 12 na dare.
Har ila yau, za a tsagaita dokar zuwa ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba karfe shida na safe.
Rundunar ta roki mutane da su guji karya dokar hukumar don gudun haduwa da fushin jami'ansu.
Dino Melaye ya yi alkawarin inganta jihar Kogi
A wani labarin, dan takarar gwamna a jihar Kogi, Sanata Dino Melaye ya yi alkawarin gina otal na alfarma a kan ruwa.
Melaye ya ce zai yi hakan ne don jawo hankalin masu zuba hannun jari da kuma yawon bude ido daga kasashen ketare.
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a jihar Kogi a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng