Zaben Jihohi: Matawalle Ya Yi Albishir Ga Ma Su Zabe, Ya Ce Su Na Dai-dai da Kowa

Zaben Jihohi: Matawalle Ya Yi Albishir Ga Ma Su Zabe, Ya Ce Su Na Dai-dai da Kowa

  • Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabukan jihohi, Gwamnatin Tarayya ta ba da tabbacin samar da tsaro mai inganci
  • Karamin Ministan Tsaro a Najeriya, Bello Matawalle shi ya ba da wannan tabbaci yayin ganawa da ‘yan jaridu a Abuja
  • Matawalle ya yi alkawarin kasancewa a ofishinsa har tsawon wannan lokaci da za a gudanar da zaben jihohin guda uku a kasar

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya bai wa ‘yan johohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi tabbacin samun ingantaccen tsaro.

Matawalle ya ba da wannan tabbaci ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna a jihohin a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

Matawalle ya ba da tabbacin samar da tsaro a zaben johohi
Matawalle ya yi martani kan tsaro a zaben jihohi. Hoto: Bello Matawalle.
Asali: Facebook

Wane alkawari Matawalle ya dauka kan tsaro a zaben?

Ministan ya yi wannan jawabi ne a yau Alhamis 9 ga watan Nuwamba yayin hira da ‘yan jaridu a Abuja, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sun samar da duk wani tsaro da ya kamata don tabbatar da gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba.

Ya ce:

“Duk wasu matakai mun dauka don hukunta duk wanda zai kawo cikas a zabukan da za a gudanar a wadannan jihohi.”

Wane tabbaci Matawalle ya bayar na tsaro a zaben?

Ya kara da cewa:

“Rundunar sojojin Najeriya za su kasance har na tsawon awanni 24, duk wanda ya ke da matsala zai iya tuntubarsu.
“Ni kai na zan kasance a cikin ofishi na har tsawon wadannan kwanaki na zabe don tabbatar da tsaron wadannan jihohi uku.”

Matawalle ya ce ya na kara bai wa ‘yan Najeriya tabbacin gudanar da zaben cikin salama ba tare da wata matsala ba, cewar NAN.

Kara karanta wannan

Satar mazakuta: tsagera sun yi wa lakcara dukan kawo wuka a jihar Arewa, 'yan sanda sun fusata

Matawalle ya yi martani kan zarge-zarge

A wani labarin, Karamin Ministan Tsaro a Najeriya, Bello Matawalle ya yi martani kan zarge-zarge da Gwamna Dauda Lawal ke yi a kansa.

Matawalle ya ce Dauda kawai nema ya ke yi ya raba shi da kujerarshi ta Minista shi ya sa ya ke ma sa bita-da-kulli.

Lawal dai na zargin Matawalle da karkatar da makudan kudade daga asusun gwamnatin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.