Filato: Bayan Tsige Ƴan Majalisar Tarayya, Kujerar Gwamnan PDP Ta Fara Tangal-Tangal a Kotu

Filato: Bayan Tsige Ƴan Majalisar Tarayya, Kujerar Gwamnan PDP Ta Fara Tangal-Tangal a Kotu

  • Kotun ɗaukaka kara mai zama a Abuja ta sanya ranar sauraron ƙarar da ɗan takarar APC ya shigar kan zaben Gwamnan Filato
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Kotun ta kori dukkan ƴan majalisar tarayya na PDP daga jihar kan rashin tsarin jam'iyya
  • Ɗan takarar APC ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun ne bayan Kotun zaɓe ta tabbatar da nasarar Gwamna Caleb Mutfwang

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta sanya ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023 a matsayin ranar sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan jihar Filato.

Kotun ta sanya ranar karban karar zaben Gwamnan jihar Filato.
Kotun Daukaka Kara Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Filato Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Kotun ta zaɓi wannan rana da zata amince da sauraron ƙarar, wadda ɗan takarar Gwamna a inuwar APC, Nentawe Yilwatda, ya ɗaukaka zuwa gabanta yana mai ƙalubalantar nasarar Gwamna Caleb Mutfwang na PDP.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Imo: Akwai yiwuwar ba za a yi zabe ba bayan an samu sabani kan muhimmin abu 1

Idan baku manta ba hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka kuma Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben Gwamna ta tabbatar masa da wannan nasara a hukuncin da ta yanke, Daily Trust ta ruwaito.

Yadda ƙarar ta kai gaban Kotun ɗaukaka ƙara

Amma duk da haka ɗan takarar APC bai haƙura ba, ya garzaya Kotun ɗaukaka kara, ya nemi ta soke nasarar PDP kuma ta ayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Filato.

Ya kafa hujjar cewa jam'iyyar PDP ba ta da halastaccen tsari kamar yadda doka da tanada, don haka ba ta cancanci tsayar da ɗan takara ba a zaben da ya gabata.

Ɗan takarar APC ya kuma shaida wa Kotun ɗaukaka ƙara a cikin bayanan ƙarar da ya shigar cewa an yi aringizon ƙuri'u kuma an saɓa wa kundin dokar zaɓe 2022 a lokacin zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Magana ra ƙare, Kotun ɗaukaka ƙara ta tsige 'yan majalisar Tarayya 3 na PDP daga Arewa

A takardar sanarwar fara zaman sauraron ƙarar, Kotun ta ce, "ranar 11 ga watan Nuwamba zamu karɓi bayanan kes din."

PDP ta rasa dukkan kujerun ƴan majalisa a Filato

Kwanan nan, Kotun ta tsige dukkan ƴan majalisun tarayya na jihar Filato bisa hujjar cewa PDP ba ta da sahihin tsari, don haka haramun ne ta tsaida ƴan takara.

Hakan ya biyo bayan rashin shirya gangamin zaɓen shugabannin jam'iyya daga matakin gundumomi zuwa jiha kamar yadda babbar Kotun jiha ta umarta tun 2021, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Emefiele ya koma cikin iyalansa

A wani rahoton kuma Daga karshe bayan hukuncin Kotu, tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya shaki iskar ƴanci.

Wannan ya biyo bayan belin da ya samu a babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja, babban lauyansa ya tabbatar da haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262