Zaben Imo: Gwamna Uzodinma da Achonu Sun Ki Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya, Bayanai Sun Fito
- Jam'iyyun siyasa 18 da za su fafata a zaɓen gwamna mai zuwa a jihar Imo sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
- Yarjejeniyar zaman lafiya ana yin ta ne domin kawar da tashe-tashen hankula kafin zaɓe, lokacin zaɓe da bayan zaɓe
- A ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023 ne za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Imo da ke yankin Kudu maso Kudu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Owerri, jihar Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma bai halarci taron da ƴan takarar gwamna a zaɓen ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, suka yi ba na rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba.
Baya ga Gwamna Uzodinma, wani fitaccen ɗan takarar da bai halarci taron ba shi ne Sanata Athan Achonu, ɗan takarar jam'iyyar Labour Party (LP).
Zaben Imo: Jam'iyyu 18 sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
Ɗan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Samuel Anyanwu, ya zo wurin taron amma ya fice bayan ya lura da rashin zuwan Uzodinma da Achonu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Premium Times ta ruwaito cewa kwamitin zaman lafiya na ƙasa (NPC) ne ya ɗauki nauyin shirya yarjejeniyar zaman lafiyan.
Duk da cewa Uzodinma, Achonu, da Anyanwu sun aika abokan takararsu, masu shirya taron sun hana su sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyan, cewar rahoton Business Day.
Haka kuma, an sanar da cewa ƴan takarar da ba su samu halartar taron ba za su iya zuwa ofishin kwamishinan ƴan sandan jihar domin sanya hannu a kan yarjejeniyar a ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba.
A nasa jawabin cikin wani faifan bidiyo, tsohon shugaban ƙasa kuma shugaban kwamitin NPC, Abdulsalami Abubakar, ya buƙaci mutane su fito su kaɗa ƙuri'unsu.
A kalamansa:
"Yana da kyau kowane mai jefa ƙuri'a ya fito domin tabbatar da cewa ya zaɓi dan takarar da yake so domin mu samu mutanen da suka dace su wakilce mu."
Ba Za a Yi Zabe a Rumfuma 40 a Imo Ba
A wani labarin kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jerin rumfunan zaɓe 40 da ba za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Imo a cikinsu ba.
Hukumar ta bayyana cewa ba za a gudanar da zaɓe a rumfunan ba ne saboda babu masu kaɗa ƙuri'a a cikinsu.
Asali: Legit.ng