Zaben Gwamnan Imo: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Wanda Zai Lashe Zabe

Zaben Gwamnan Imo: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Wanda Zai Lashe Zabe

  • Apostle Ako Anthony ya bayyana abun da ya hango dangane da zaben gwamna mai zuwa a jihar Imo a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba
  • A hasashen Apostle Anthony, jam'iyyar APC da dan takararta, Hope Uzodimma ne za su yi nasara a zaben
  • Uzodimma shine gwamnan jihar mai ci kuma yana neman zarcewa wanda zai ba shi damar jagorantar kasar har zuwa 2028

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Owerri, jihar Imo - Apostle Ako Anthony na cocin 'Mountain of Christ Prayer Ministry International' ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC ce za ta yi nasara a zaben gwamna mai zuwa a jihar Imo.

Yayin wata shirin kai tsaye a Facebook a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, wanda Legit ta gano, Apostle Anthony ya ce Hope Uzodimma, dan takarar jam'iyyar APC zai lallasa Samuel Anyanwu, Athan Achonu, da sauransu.

Kara karanta wannan

“Na hango zubar jini”: Malamin addini ya yi hasashe mai ban tsoro game da zaben gwamnan Kogi

Anyanwu ne ke rike da tutar jam'iyyar PDP, yayin da Achonu ke wakiltar jam'iyyar LP.

Malamin addini ya yi hasashen wanda zai lashe zaben gwamnan Imo
Zaben Gwamnan Imo: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Wanda Zai Lashe Zabe Hoto: Hope Uzodimma, Senator Athan Nneji Achonu, Ezekwe Uche Ezekwe
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'APC za ta lashe jihar Imo': Apostle Anthony

A cewar Apostle Anthony, Uzodimma zai dawo da kuri'unsa ta kowani hali.

Ya ce:

"Ina so na ce, a badini, zaben jihar Imo ya kamata ya zama na jam'iyyar LP.
"APC za ta kwato jihar Imo ta kowani hali."

Legit Hausa ta rahoto cewa an sanya ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaben gwamnan jihar Imo na 2023.

Malami ya yi hasashen makomar zaben Kogi

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rafoto a baya cewa Eneojo Suleman, babban fasto a cocin Hill of Shalom Global Ministry, ya bayyana cewa zaben gwamna da za a yi a jihar Kogi "zai kasance mai zafi". Fasto Sulam ya bayyana cewa ya hango kazamin karo a yayin zaben.

Malamin addinin ya kuma yi hasashen cewa tsakanin Murtala Ajaka (Muri) na jam'iyyar SDP da dan takarar jam'iyyar APC mai mulki, Ahmed Ododo, ne wani zai lashe zaben da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba. Fasto Suleman ya kasance haifaffen dan jihar Kogi ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng