Babu Sunan Wike Yayin da Babachir Lawal Zayyano Ministocin Tinubu da Suka Cancanta

Babu Sunan Wike Yayin da Babachir Lawal Zayyano Ministocin Tinubu da Suka Cancanta

  • Tsohon SGF, Babachir Lawal ya bayyana ra’ayinsa game da ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa
  • Ɗan siyasar ya ce ministoci biyu ne kawai cikin ministoci 46 da ke ƙarƙashin gwamnatin Tinubu wadanda za su yi abin a zo a gani
  • Ya ƙara da cewa ya kira ministocin biyu tare da taya su murnar naɗin da Shugaba Tinubu ya yi musu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya bayyana wani abun ban mamaki game da ministoci 46, da ke aiki a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise News a ranar Laraba 8 ga watan Nuwamba, Lawal ya bayyana cewa ministoci biyu ne kawai daga cikin ministoci 46 suka cancanta.

Kara karanta wannan

Kogi: "Ni ake nema a kashe" Ɗan takarar Gwamna ya tona shirin Gwamnan APC a jihar arewa

Babachir ya yi magana kan ministocin Tinubu
Babachir Lawal ya bayyana ministocin Tinubu da suka cancanta Hoto: Babachir Lawal, Wale Edun, Governor David Nweze Umahi
Asali: Facebook

Ya cigaba da cewa, tsohon gwamnan jihar Ebonyi kuma yanzu ministan ayyuka, David Umahi da Wale Edun, ministan kuɗi, su ne kawai ministocin da ya ke da tabbacin cewa aka sanya su a inda ya dace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Lawal ya ke ganin sun cancanta?

Lawal ya ƙara da cewa ya sanar da su sannan kuma ya taya su murnar naɗin da aka yi musu.

Babachir Lawal ya bayyana cewa:

"A bisa sanina da wasu abokan Shugaba Tinubu, na san muƙamin da kowa zai samu lokacin da ya sanar da majalisar ministocinsa 46."
"Ina so in tunatar da ku cewa mun kasance abokai da Bola Tinubu shekaru da yawa kuma na san mutanen da ke tare da shi."
"Kuma ina da yaƙinin cewa bisa ga sanina na wasu abokansa, na yi tunanin wanda zai samu muƙami da abin da zai yi."

Kara karanta wannan

Datti Baba-Ahmed abokin takarar Obi ya bukaci Tinubu da Shettima su yi murabus, ya bayyana dalilansa

"Lokacin da ya sanar da majalisar ministocinsa 46, maganar gaskiya mutum biyu ne kawai na yarda sun cancanta, sannan na kira waɗannan mutum biyun a waya na taya su murna sannan na gaya musu cewa an sanya su inda ya dace."
"Mutum na farko shi ne Dave Umahi, wanda shi ne ministan ayyuka sannan kafin ya zama gwamna injiniya ne mai gina tituna. Don haka na yi masa kallon wanda aka sanya a inda ya dace. Na taya shi murnar naɗin da aka yi masa.
"Mutum na biyu da na ke ganin an sanya shi a inda ya dace shi ne ministan kuɗi, Wale Edun, shi ma na taya shi murna."

APC Ta Yi Wa Babachir Tonon Silili

A wani labarin kuma, jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta yi Babachir Lawal raddi kan iƙirarinsa na cewa Peter Obi ne ya lashe zaɓen Shugaban ƙasa.

APC ta bayyana cewa Babachir yana jin haushi ne kawai saboda ya kasa samun mataimakin shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng