Magana Ta Kare, Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tsige Ƴan Majalisar Tarayya 3 Na PDP Daga Jihar Arewa
- Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin korar ƴan majalisun tarayya na PDP uku daga majalisar wakilan tarayya
- Yayin yanke hukunci ranar Talata, Kotun mai zama a Abuja ta ce PDP ta saɓa umarnin Kotu, don haka duk ƙuri'un da ta samu basu da amfani
- Tun da farko Kotun zaɓe ta tsige ƴan majalisun bisa hujjar cewa takararsu ba ta inganta ba a inuwar jam'iyyar PDP
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja, a hukuncin da ta yanke lokuta daban-daban ranar Talata, ta tabbatar da tsige ƴan majalisar wakilan tarayya uku daga jihar Filato.
Dukkan ƴan majalisun uku da suka rasa kujerunsu sun samu nasara ne ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2023, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Kotun ta amince da korar su daga majalisar wakilan tarayya bisa rashin halascin takarar da suka tsaya karƙashin inuwar jam'iyyar PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin yan majalisun da kotu ta tsige
Waɗanda Kotun ɗaukaka ƙara ta yi na'am da tsige su sun haɗa da, Peter Gyendeng mai wakiltar mazaɓar Barkin-Ladi/Riyom a majalisar wakilan tarayya.
Sauran ƴan majalisun guda biyu su ne, Musa Bagos, mai wakiltar mazaɓar Jos ta kudu/Jos ta gabas da kuma wanda karo na farko kenan da ya ci zaɓe, Beni Lar, mai wakiltar Langtang ta arewa/Langtang ta kudu.
Meyasa Kotu ta amince da wannan hukunci?
Kotun ɗaukaka ƙara ta ce jam’iyyar PDP ta saba umarnin kotu, lokacin da ta dauki nauyinsu a matsayin ‘yan takararta na zaben ‘yan majalisar tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
A cewar kotun, PDP ta yi watsi da umarnin Kotu a kara mai lamba PLD/J/304/2021, inda aka umarci ta gudanar da sabon taro a dukkanin kananan hukumomi 17 na jihar Filato.
Kotun ta bayyana cewa maimakon bin wannan umarni, jam’iyyar PDP ta ci gaba da harkokinta, ta tsaida ‘yan takarar da suka ci zabe a mazabu daban-daban.
Bisa haka kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron korafin zabe ta jihar Filato karkashin jagorancin Mai shari’a Mohammed Tukur, rahoton The Nation.
Tun farko, Kotun zaben ta yanke cewa tun da kuri'un da PDP ta samu sun zama mara amfani, ƴan takarar sauran jam'iyyu da suka zo na biyu a mazaɓun ne suka ci zaɓe.
Ɗan takarar SDP ya yi zargin ana neman kashe shi
A wani rahoton kuma Murtala Ajaka ya zargi Gwamna Yahaya Bello da amfani da wasu jami'an tsaro domin cimma burinsa na raba shi da duniya.
Ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a inuwar SDP ya ce manufar harin da aka kai Dekina shi ne a kashe shi amma ya tsallake.
Asali: Legit.ng