Hukuncin Kotun Koli: Abubuwa 2 da Atiku Zai Fara Yi Bayan Rashin Nasararsa Ga Shugaba Tinubu

Hukuncin Kotun Koli: Abubuwa 2 da Atiku Zai Fara Yi Bayan Rashin Nasararsa Ga Shugaba Tinubu

Barista Titilope Anifowoshe, ta shawarci ɗan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, da ya fara duba matakin da zai ɗauka bayan rashin nasararsa a kotun ƙoli.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Anifowoshe, masaniyar shari’a kuma marubuciya, wacce ta zanta da Legit.ng kan mataki na gaba da tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai ɗauka.

An ba Atiku Abubakar shawara
An ba Atiku Abubakar shawara bayan rashin nasararsa a kotun koli Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Ta bayyana cewa Atiku zai iya shiga gwamnatin Shugaba Tinubu a halin yanzu ko kuma ya koma ya sake sabon lale kafin zuwan zaɓen 2027.

Atiku na iya shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 inji Anifowoshe

Shahararriyar masaniyar dokar ta bayyana cewa zaɓen 2023, ba shi ba ne karon farko da Atiku ya jiyo ƙamshin yin nasara ba, tun lokacin da ya fara tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun koli: An ba Peter Obi shawarar abin da ya kamata ya yi wa Shugaba Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike ya bayyana cewa Atiku ya shafe shekaru 30 yana neman zama shugaban ƙasar Najeriya, wanda na baya-bayan nan shi ne a 2023 inda ya yi rashin nasara a zaɓe da kuma kotu.

Atiku ya goyi bayan Tinubu ko kuma ya shirya zaɓen 2027

Da ta ke magana kan mataki na gaba da dan takarar PDP zai iya ɗauka bayan rashin nasararsa a kotun ƙoli kwanan nan, Anifowoshe ta cigaba da cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar yana da damar tsayawa takara a kowane lokaci.

A kalamanta:

"Alhaji Atiku yana da ƴancin tsayawa takarar shugaban ƙasan a Najeriya, idan har yana jin cewa yana da abin da ya kamata ya tafiyar da mulkin Najeriya, ko dai zai iya haɗa kai da gwamnatin da ke mulki a matsayinsa na ɗan ƙasa, ko kuma ya koma ya sake yin shirin yin takara nan da shekara huɗu domin samun mafi yawan ƙuri'u."

Kara karanta wannan

"Ba zan taba daina kiran Tinubu dillalin kwayoyi ba", Datti Baba-Ahmed ya bayar da dalili

"Wannan ba shi ne karon farko da ya kusa lashe zaɓen shugaban ƙasa ba. Saboda haka zai iya cigaba da gwada sa'arsa har sai ya yi nasara."

Atiku ya fara neman tikitin takarar shugaban ƙasa a ƙarkashin jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a jamhuriya ta uku.

Ya zuwa shekarar 2023, Atiku mai shekaru 77 ya yi yunƙurinsa na neman shugabancin ƙasa karo na bakwai ba tare da yin nasara ba.

Lauya Ya Shawarci Atiku da Peter Obi

A wani labarin kuma, shahararren lauyan kare haƙƙin bil Adama, Enibehe Effiong, ya ba Atiku Abubakar da Peter Obi shawara bayan rashin nasararsu a kotun ƙoli.

Effiong ya buƙaci ƴan siyasar biyu da su mayar da hankali wajen gudanar da ayyukan adawa na bin diddigin ayyukan gwamnatin Shugaba Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng