Kotun Ɗaukaka Kara Ta Gama Aiki, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Ɗiyar Tsohon Gwamna a Zaben 2023
- Ibori-Suenu Erhiatake, ɗiyar tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, ta samu nasara a Kotun ɗaukaka kara mai zama a jihar Legas
- Kotun ta tabbatar da nasarar Honorabul Erhiatake a matsayin wadda ta lashe zaɓen ƴar majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Ethiope
- Alƙalan Kotun sun bayyana cewa ƴar takarar ta PDP ta shigar da karar da ta cancanta, bisa haka ta soke hukuncin Kotun zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Lagos - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a jihar Legas ta tabbatar da nasarar Honorabul Ibori-Suenu Erhiatake (PDP) a matsayin halastacciyar ƴar majalisar tarayya daga jihar Delta.
Erhiatake ta jam'iyyar PDP ta samu nasarar lallasa manyan abokan adawarta a mazaɓar Ethiope ta tarayya, Ben Rolands Igbakpa da Mista Halims Ahoda na jam'iyyun NNPP da APC.
Kwamitin alkalai uku da suka haɗa da mai shari'a Festus Ogbuinaya, Mai shari'a Senchi, da kuma mai shari'a Waziri ne suka yanke hukunci a ƙarar ranar Talata a jihar Legas.
Ibori-Suenu ta kasance diyar tsohon gwamnan jihar Delta kuma jagoran jam'iyyar PDP a jihar, Cif James Onanefe Ibori, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun daukaka kara ta ce karar da ƴar takarar PDP ta ɗaukaka zuwa gabanta ta yi dai-dai kuma ta gamsu da hakan, inda ta yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke.
Tun da farko, hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta ayyana ɗiyar tsohon gwamnan a matsayin wacce ta lashe zaɓen mamba mai wakiltar mazaɓar Ethiope a majalisar wakilan tarayya.
Bisa rashin gamsuwa da sakamakon, abokan adawarta suka shigar da ƙara a gaban Kotun zaɓe inda suka kalubalanci nasarar da ta samu.
Ɗiyar Ibori ta maida martani kan nasarar da ta samu
Da take maida martani a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, ƴar majalisar wakilai Erhiatake ta ayyana hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara matsayin nasara daga Allah.
Ta kuma yaba da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke tana mai cewa dimokradiyya na nan daram.
NLC da TUC sun kira taron NEC
A wani rahoton kuma Ƙungiyar kwadago NLC da takwararta TUC sun kira taron majalisar zartarwa (NEC) kan wasu muhimman batutuwa.
Daga cikin abin da taron zai maida hankali harda yiwuwar shiga yajin aiki biyo bayan cin mutuncin da aka yi wa shugaban NLC.
Asali: Legit.ng