Miyagu Sun Kai Hari Gidan Babban Jigon PDP Kuma Tsohon Kwamishina, Sun Jefa Bama-Bamai

Miyagu Sun Kai Hari Gidan Babban Jigon PDP Kuma Tsohon Kwamishina, Sun Jefa Bama-Bamai

  • 'Yan daban siyasa sun kai farmaki da bama-bamai a gidan tsohon kwamishina kuma jigon jam'iyyar PDP a jihar Baylesa, Chief Diekivie Ikiogha
  • Rahotanni sun bayyana cewa ba bu wanda harin ya shafa amma ƴan daban sun jikkata wasu mutum biyu a wani wurin daban a Yenagoa
  • Hukumar yan sanda reshen jihar Bayelsa ta ce zata gudanar da binciken kan abin da ya afku kafin ta fitar da sanarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bayelsa - Wasu tsageru da ake zargin ƴan daban siyasa ne sun kai hari gidan wani babban jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Bayelsa, Chief Diekivie Ikiogha.

Yan daba sun kai farmaki gidan jigon PDP.
Yan Daba Sun Farmaki Gidan Babban Jigon PDP a Jihar Bayelsa, Mutum 2 Sun Jikkata Hoto: punchng
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Punch ta tattaro, ƴan daban sun kai harin gidan jigon da ke Unguwar Kpansia a Yenagoa, babban birnin jihar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane a wurin Maulidi, 'yan bindiga sun ƙara kai ƙazamin hari a jihar Katsina

An tattaro cewa maharan sun jefa ababen fashewa da ake kyautata zaton nakiya ce kan ginin gidan jigon jam'iyyar PDP yayin harin na yau a Bayelsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma wasu mutum biyu da ba a gano bayanansu ba har yanzu sun ji raunuka yayin da wasu ƴan baranda suka farmake su a Unguwar Apolo duk cikin Yenagoa.

Yadda yan daban suka kai hari da bama-bamai

Babu wanda ya samu rauni a harin da aka kai a gidan Mista Ikiogha, amma tagar da ke kusa da wurin da bam din ya fado a cikin harabar gidan ta yi kaca-kaca.

Yayin da wakilin jaridar ya ziyarci gidan jigon PDP da aka kai wa hari, ya ga ramin da Bam ɗin ya tashi a wurin da tagar da ta lalace sanadim fashewar bam.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari Abuja, sun tafka ɓarna yayin da suka yi garkuwa da mutane

Wasu mazauna Unguwar sun bayyana cewa sun ji sautin ƙara mai ƙarfi ta fashewar wani abu daga cikin gidan da misalin ƙarfe 2:00 na safiyar nan.

"Na ji wani sautin fashewa mai ƙarfi daga ginin da misalin karfe biyu na daren jiya. Amma ban san abin da ya haifar da hakan ba, ”in ji wani mazauni, wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Sai dai ba a samu jin ta bakin jigon, Mista Ikiogha ba, wanda ya taɓa rike muƙamin kwamishinan noma da kuma shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Bayelsa.

Dan siyasar ya koma jam’iyyar PDP ne a makon jiya, shekaru da dama bayan ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC), The Nation ta ruwaito.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Asinim Butswat, ya ce zai binciki abin da ya faru kana ya dawo gare mu amma har yanzu shiru.

Mahara sun kashe mutane a Katsina

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga babbar matsala, masu ruwa da tsakin PDP sun goyi bayan Ministan Tinubu

A wani rahoton na daban Miyagun ƴan bindiga sun ƙara kashe mutane a kauyen Sayaya da ke ƙaramar hukumar Matazu a jihar Katsina ranar Litinin.

Wannan harin na zuwa ne kwana ɗaya tal bayan mahara sun kai hari wurin taron Maulidi a ƙaramar hukumar Musawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262