INEC Ta Bi Umarnin Kotun Ɗaukaka Kara, Ta Yi Gyara a Jerin Ƴan Takarar Gwamnan Jihar Bayelsa
- Hukumar zabe ta ƙasa INEC ta yi gyara a jerin sunayen ƴan takarar da zasu fafata a zaben gwamnan jihar Bayelsa
- A sabon jerin sunayen da INEC ta buga a shafinta, ta ƙara sunan ɗan takarar APC, Timipre Sylva da mataimakinsa, Maciver Joshua
- Hakan ya biyo bayan hukuncin Kotun ɗaukaka kara wacce ta jingine umarnin babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bayelsa - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kara sunan Timipre Sylva a cikin jerin sunayen ‘yan takarar da za su fafata a zaben gwamnan jihar Bayelsa.
A ranar 9 ga watan Yuni ne INEC ta fitar da jerin sunayen 'yan takarar da da zasu fafata a zaben Bayelsa, ciki har da Sylva, tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Minista.
Amma a ranar 10 ga Oktoba, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta hana Sylva, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) shiga zaben, The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Kotu ta hana Sylva takara da farko?
Kotun ta ce Sylva, wanda aka rantsar sau biyu kuma ya yi mulki na tsawon shekaru biyar a matsayin gwamnan jihar, zai karya kundin tsarin mulkin 1999 idan ya sake tsayawa takara.
Yayin biyayya ga hukuncin kotun, INEC ta cire sunan Sylva daga cikin sunayen ‘yan takarar da za su fafata a zaben gwamnan wanda za a yi ranar Asabar mai zuwa.
Amma a ranar 31 ga watan Oktoba, wata kotun daukaka kara a Abuja ta soke hukuncin hana Sylva takara a zaɓen.
INEC ta bi sabon umarnin Kotu
Sakamakon haka, INEC ta ƙara sunan Sylva da abokin gaminsa, Maciver Joshua, a sabon jerin sunayen ƴan takarar da ta wallafa a shafinta na yanar gizo-gizo ranar Litinin.
Sanarwar da ke tare da sabon jerin sunayen ta ce an yi gyaran ne domin biyayya ga hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Sanarwan ta ce:
“Bisa tanadin sashe na 287 na kundin tsarin Mulkin na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, hukumar za ta aiwatar da umarnin Kotu kan ‘yan takara daga jam’iyyun siyasa a Jihar."
APC ta ƙara takaita PDP a jihar Edo
A wani rahoton kuma Tsohon ministan ayyuka da tsohon ɗan takarar gwamna sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC a jihar Edo.
Jiga-jigan biyu, Arch Mike Onolememen da Gideon Ikhine tare da magoya bayansu sun samu tarba mai kyau ranar Litinin.
Asali: Legit.ng