Ganduje Ya Yi Kamu, Tsohon Minista da Ɗan Takarar Gwamna Sun Kara Yi Wa PDP Lahani

Ganduje Ya Yi Kamu, Tsohon Minista da Ɗan Takarar Gwamna Sun Kara Yi Wa PDP Lahani

  • Tsohon ministan ayyuka da tsohon ɗan takarar gwamna sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC a jihar Edo
  • Jiga-jigan biyu, Arch Mike Onolememen da Gideon Ikhine tare da magoya bayansu sun samu tarba mai kyau ranar Litinin
  • Jagoran APC na yankin Esan, Cecil Esekhaigbe, ya ce sauya sheƙar mutanen na nuni da cewa APC zata kwace mulki a 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Ministan ayyuka a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, GoodLuck Jonathan, Arch Mike Onolememen, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC a Edo.

Mista Gideon Ikhine.
Zaben Edo: Tsohon Ministan Ayyuka da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Koma APC Hoto: punchng
Asali: UGC

Haka kuma tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, wanda ya janye wa Gwamna Obaseki bayan ya baro APC zuwa PDP a 2020, Gideon Ikhine, ya bi sahu zuwa APC.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga babbar matsala, masu ruwa da tsakin PDP sun goyi bayan Ministan Tinubu

Waɗan nan jiga-jigan biyu tare da magoya bayansu sun tattara sun canza sheƙa zuwa APC, inda suka samu tarba mai kyau ranar Litinin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagoran APC a yankin Esan, Janar Cecil Esekhaigbe mai rtaya ne ya tarbi masu sauya sheƙar da magoya bayansu a garun Uromi, hedkwatar ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas.

Da yake jawabi, Jigon ya bayyana cewa shigowar waɗannan ƙusoshin siyasar cikin APC wata alama ce da ke nuna jam'iyyar zata samu nasara a zaɓen gwamna mai zuwa a 2024.

Ya kuma ƙara da cewa shiyyar Sanatan yankin ne zata fidda gwamnan jihar Edo na gaba.

Esekhaigbe ya ce:

"Wadannan manyan mutane ne, kuma sanannu ne a Najeriya da ma’abota siyasa don haka matakin na nuna jam’iyyar APC ce ta dace mutane su runguma."

Kara karanta wannan

Makinde: Gwamnan PDP ya ciri tuta, ya yi ƙarin albashi mai tsoka ga ma'aikata da 'yan fansho

"Sauya shekarsu na da muhimmanci saboda yayin da muke tunkarar 2024, alamu sun fito fili cewa Esan ce zata fidda sabon gwamna na gaba. Zamu haɗu mu matsa kuma zamu ci nasara da yardar Allah."

Meyasa suka koma APC?

A nasa jawabin, Mista Ikhine, ya bayyana cewa ya yanke shawarar shiga APC ne domin kwace gwamnatin jihar Edo a zaɓe na gaba.

"Hakan zai nuna wa al'umma su fahimci cewa zuwa 2024, jam'iyyar APC za ta mamaye gidan gwamnati da ke Osadebe. APC na zaune lafiya babu wata rigimar cikin gida," in ji shi.

Wani jigon APC, Usman Lawal, ya shaida wa Legit Hausa cewa tabbas jam'iyyar su tana zawarcin ƴan adawa a shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

"Wannan ba abun mamaki bane, domin APC tun bayan zuwan Ganduje ta fara shirin tunkarar zabe na gaba, na san a nan yanki na Ɗanja a jihar Katsina, muna kokarin shawo kan wasu su shigo a dama da su."

Kara karanta wannan

Shugabannin NNPP a Arewa maso Yamma sun yi zama kan batun korar Kwankwaso a jam'iyya

Ya faɗa wa wakilin mu cewa nan gaba jiga-jigan jam'iyyu harda masu riƙe da madafun iko zasu sauya sheƙa zuwa APC gabanin babban zaɓe mai zuwa.

Mahaifin Gwamna Soludo Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani rahoton kuma Allah ya yi wa mahaifin Gwamna Soludo na jihar Anambra rasuwa da sanyin safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, 2023.

Sakataren watsa labaran gwamnan, Christian Aburume, ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne bayan fama da jinya ta ɗan lokaci ƙanƙani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262