Daga Karshe Peter Obi Ya Bayyana Matsayarsa Kan Hukuncin Kotun Koli
- Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Labour Party (LP), ya bayyana matsayarsa kan hukuncin kotun ƙoli
- Obi ya yi nuni da cewa hukuncin kotun ƙoli ba shi ne zai kawo ƙarshen tafiyarsa ta gina sabuwar Najeriya ba
- Ɗan takarar ya yi nuni da cewa yanzu jam'iyyar LP ta tsunduma adawa inda za su sake gina ta da farfaɗo da ita
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi ya amince da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke wanda ya tabbatar da zaɓen shugaban kasa Bola Tinubu.
Peter Obi, ya bayyana cewa hukuncin ba shi ba ne zai kawo ƙarshen tafiyar ƴan 'Obedients' ba, cewar rahoton The Nation.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce tun da an kawo ƙarshen shari’a, yanzu jam’iyyar Labour Party tana ɓangaren adawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa har yanzu ƙudirinsa na sabuwar Najeriya yana nan daram.
Obi ya yi magane ne dai kan hukuncin kotun ƙolin a wani taron manema labarai a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba a birnin tarayya Abuja.
Kotun koli a ranar 26 ga Satumba, ta amince da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke a ranar 6 ga Satumba, inda ta tabbatar da Tinubu a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.
Kotun mai alƙalai bakwai a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a John Inyang-Okoro, ta yi watsi da ƙararrakin da ɗan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya zo na biyu a zaɓen, da Obi wanda ya zo na uku a zaɓen suka shigar.
Wane mataki Peter Obi zai ɗauka na gaba?
A kalamansa:
“A watanni masu zuwa za mu gina jam’iyyar, za mu ƙara karfi. Za mu gina waɗannan matasa. Za mu fito da ƙarfinmu da himma domin samun sabuwar Najeriya.
"Ba mu san abin da zai faru gobe ba. Abin da mu ka mayar da hankali a yanzu shi ne mun yi abin da ya dace domin amfanin Najeriya"
Lauya Ya Shawarci Peter Obi da Atiku
A wani labarin kuma, shahararren lauyan kare haƙƙin bil Adama, Inibehe Effiong, ya ba Peter Obi da Atiku Abubakar shawara kan hukuncin kotun ƙoli.
Lauyan ya ce akwai bukatar yan takarar biyu su mayar da hankali wajen gudanar da ayyukan adawa na bin diddigin ayyukan gwamnatin Shugaba Tinubu.
Asali: Legit.ng