“Ina Alfahari Matuka”: Tinubu Ya Caccaki Atiku da Obi Yayin da Yake Jawabi Ga Ministocinsa

“Ina Alfahari Matuka”: Tinubu Ya Caccaki Atiku da Obi Yayin da Yake Jawabi Ga Ministocinsa

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi martani a kan hukuncin kotun koli da ya yi watsi da karar da Atiku Abubakar da Peter Obi suka daukaka
  • Yayin da yake jawabi ga Nyesom Wike da sauran ministoci, shugaban kasar ya ce yana matukar alfahari da kansa tunda ya kayar da abokan hamayyarsa a zaben da kotu
  • Tinubu ya jaddada jajircewarsa na yiwa Najeriya hidima sannan ya tunatar da ministocinsa game da alakawarin da gwamnatinsa ta daukarwa yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya caccaki Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP bayan ya yi nasara a doguwar shari'ar da suka yi da shi a kotun koli.

Kara karanta wannan

Murna yayin da Faransa za ta dawo da makudan kudin da Abacha ya sace

Da yake jawabi ga Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja da sauran mambobin majalisarsa a wani bidiyo da Legit Hausa ta gano, shugaban kasar ya ce yana alfahari da kayar da Atiku da Obi da ya yi a zabe da kotu.

Tinubu ya yi martani ga hukuncin kotun koli
“Ina Alfahari Matuka”: Tinubu Ya Caccaki Atiku da Obi Yayin da Yake Jawabi Ga Ministocinsa Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi
Asali: Twitter

A ranar Laraba, 1 ga watan Maris, Mahmoud Yakubu, shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ya ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku da Obi sun tunkari kotun koli kan nasarar da Tinubu ya yi a kotun zabe

Atiku da Obi sun yi watsi da sakamakon zaben sannan suka shigar da kararraki kan nasarar shugaban kasa Tinubu a kotun zaben shugaban kasa amma sai kotun ta yi watsi da kararrakinsu saboda rashin inganci.

Kara karanta wannan

Nasarar Tinubu a Kotun Koli: APC ta aikawa Atiku, Peter Obi sakon gaggawa

Masu karar sun tunkari kotun koli don daukaka kara kan hukuncin kotun zaben yayin da Atiku ya yi tattaki har Amurka don neman bayanan karatun Tinubu a jami'ar jihar Chicago don tabbatar da cewar shugaban kasar ya yi badakalar takardarsa.

Sai dai kuma abun ya tashi a tutar babu don kotun kolin ta yi watsi da kararrakinsu saboda rashin inganci.

A cikin bidiyon, an jiyo Tinubu yana cewa:

"Ina alfahari da kaina. Na je zabe, Na lashe zabe da goyon bayanku. Sun kai ni kotu, Na yi nasara."

Kalli bidiyon a kasa:

Tinubu zai shilla kasar Saudiyya

A wani labarin kuma, mun ji cewa mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa, Shugaba Tinubu zai kai ziyara kasar Saudiyya domin halartar taro don jawo hankulan ‘yan kasuwa da masu zuba hannun jari zuwa Najeriya.

Wannan na zuwa ne a lokacin da hadimin na Tinubu ke zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng