APC da LP Sun Gamu da Cikas, Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Ƴan Majalisar Tarayya 2

APC da LP Sun Gamu da Cikas, Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Ƴan Majalisar Tarayya 2

  • Kotun ɗaukaka kara ta maida wa Amobi Ogah na LP kujerarsa ta mamban majalisar wakilan tarayya daga jihar Abiya
  • Ta kuma rushe zaɓen ɗan majalisar Udenu/Igboeze, Denis Agbo na LP, inda ta umarci INEC ta canza zaɓe a mazabar cikin kwanaki 90
  • Da farko, Kotun zaɓe ta kwace kujarar Ogah, amma ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara inda ya kalubalanci hukuncin

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a jihar Legas ta soke hukuncin da Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen ƴan majalisa tarayya da na jiha ta yanke.

Kotun ta jingine wannan hukunci, wanda ya rushe nasarar mamba mai wakiltar mazaɓar Isikwuato Umunneochi daga Abia a majalisar wakilan tarayya, Amobi Oga.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar ɗan majalisar tarayya daga Kaduna

Amobi Ogah ya kwato nasararsa a Kotun daukaka kara.
Dan Majalisar Tarayya Na LP Ya Dawo da Nasararsa a Kotun Daukaka Kara Hoto: Hon Amobi Ogah
Asali: Facebook

Idan baku manta ba a watan Satumba, Kotun zaɓe mai zama a Umuahia ta tsige Ogah daga kujerar ɗan majalisar, kana ta ayyana Nkiruka Onyejeocha ta APC a matsayin wadda ta ci zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nkiruka Onyejeocha, ita ce ƙaramar ministar kwadago a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wane hukunci Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke?

Bayan haka ne Honorabul Ogah na jam'iyyar LP ya garzaya Kotun ɗaukaka ƙara ya kalubalanci wannan hukuncin, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Da take yanke hukunci jiya Jumu'a, Kotun ɗaukaka kara ta jingine hukuncin Kotun zaɓe, ta tabbatar da nasarar Ogah na LP a zaben watan Fabrairu.

A cewar Kotun, ƙarar da ɗan takarar Labour Party ya ɗaukaka zuwa gabanta ta yi daidai kuma ta gamsu da hujjoji da bayanansa, kana ta soke hukuncin da ƙaramar Kotu ta yi.

Kara karanta wannan

Bayan kwace kujerar Sanatan APC, Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan zaɓen Sanatan Kogi ta gabas

Kotun ta tsige ɗan majalisar tarayya na LP

Haka nan kuma Kotun ɗaukaka ƙara mai zama Legas ta tsige ɗan majalisa mai wakiltar Udenu/Igboeze daga jihar Enugu a majalisar tarayya, Denis Agbo, na Labour Party.

Kotun ta tsige Agbor daga kujerar mamban majalisar tarayya kana ta umarci hukumar zaɓe INEC ta shirya sabon zaɓe cikin watanni uku masu zuwa.

Da ta yanke hukunci ta Zoom, ta ce karar da dan takarar APC, Oby Ajih, wanda ya nemi a tilasta wa INEC ta shirya sabon zaɓe tsakanin bangarorin da abin ya shafa ta cancanta.

Gwamna Fubara ya bada hakuri

A wani rahoton kuma Gwamna Similanayi Fubara ya roki afuwar mazaunan jihar Ribas bisa rikicin siyasar da ya ɓarke a jihar a baya-bayan nan.

Ya kuma bayyana abin da ya kai shi majalisar dokokin jihar Ribas da kuma yadda aka yi yunkurin tsige shi daga mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel