Zaben Bayelsa: Tashin Hankali Yayin da Yan Daba Suka Farmaki Yan PDP, An Kashe 1, Wasu Sun Jikkata
- Yan daba sun farmaki wasu mambobin jam'iyyar PDP a karamar hukumar Nembe ta jihar Bayelsa
- Harin na zuwa ne mako guda kafin zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023
- A cewar rahoto, an kashe dan PDP daya sannan wasu da dama sun jikkata a garin Ogbolomabiri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Bayelsa - Yan daban siyasa sun farmaki mambobin jam'iyyar PDP a karamar hukumare Nembe da ke jihar Bayelsa.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, yan daban sun kashe wani mai suna Timi Biriyai Macdonald sannan sun jikkata wasu da dama ciki harda jigon jam'iyyar, Diepreye Akrisia.
Shugaban PDP a jihar ya yi ikirarin cewa yan daban da ake zargin magoya bayan APC ne sun farmaki mambobinsu a garin Ogbolomabiri da ke karamar hukumar Nembe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, sun bayyana harin a matsayin “mummuna” kuma na rashin hankali, kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.
"A kan haka, jam'iyyar PDP din ta bukaci yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar da su yi bincike ba tare da bata lokaci ba sannan su kama tare da hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan hari na rashin hankali kan bayin Allah da basu ji ba basu gani ba, don ya zama izina ga saura a yayin zaben na ranar 11 ga watan Nuwamba."
LP ta marawa Dino baya a zaben Kogi
A wani labarin, mun ji cewa jam'iyyar Labour Party ta tsayar da dan takarar jam'iyyar People Democratic Party (PDP) Sanata Dino Melaye a matsayin dan takararta a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, a jihar Kogi.
Melaye ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, a wata wallafa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @_dinomelaye.
Tsohon dan majalisar tarayyar ya bayyana cewa an kulla kawancen ne domin tsame jihar Kogi daga duhun gwamnatin APC karkashin jagorancin Gwamna Yahaya Bello.
Asali: Legit.ng