An Maka Shugaba Tinubu a Kotu Saboda Wani Dalili 1 Tak

An Maka Shugaba Tinubu a Kotu Saboda Wani Dalili 1 Tak

  • Jam'iyyar PDP a Akwa Ibom ta maka Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a kotu kan nada dan jam'iyyarsa ta APC, a matsayin kwashinan hukumar zabe ta kasa (INEC)
  • Shugaba da sakataren PDP na jihar Aniekan Akpan da Harrison Ekpo, ne suka shigar da karar a babbar kotun tarayya, Abuja
  • Babbar jam'iyyar adawar Najeriya na kalubalantar zabar Etekamba Umoren da shugaban kasar ya yi a matsayin kwamishinan zabe na jihar Akwa Ibom

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Uyo, jihar Akwa Ibom - Aniekan Akpan, shugaban PDP a jihar Akwa Ibom da sakataren jam'iyyar, Harrison Ekpo, sun maka Shugaban Kasa Bola Tinubu a kotu.

An kuma maka shugaban majalisar dattawa, Godswill Obot Akpabio ma a kotun, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugabannin NNPP a Arewa maso Yamma sun yi zama kan batun korar Kwankwaso a jam'iyya

An maka Shugaban kasa Tinubu a kotu
An Maka Shugaban Kasa Bola Tinubu a Kotu Saboda Wani Dalili 1 Tak Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Nadin Kwamishinan Zabe: Jiga-jigan PDP sun maka Tinubu a kotu

An maka jiga-jigan na APC biyu a kotu ne kan nadin Etekamba Umoren, a matsayin kwamishinan zabe (REC) na jihar ta kudu maso kudu, jaridar Business Day ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta ayyana cewa Umoren bai cancanci a nada shi a matsayin kwamishinan zabe ba, ganin cewa shi dan jam’iyyar APC ne.

A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/146/2023 da suka shigar a gaban babbar kotun tarayya, Abuja, masu karar sun zayyana bukatunsu da suka hada da:

“Cewa wanda ake tuhuma na 1 (Tinubu) ba zai iya gabatar da wanda ake kara na 3 (Umoren) ga wanda ake kara na 2 (Majalisar Dattawa) don tabbatar da shi a matsayin REC na Akwa Ibom ba.

Kara karanta wannan

Kano: Kujerar Majalisar Tarayya da kotu ta karbe ya dawo hannun NNPP a karshe

"Cewa nadin wanda ake kara na 3 a matsayin REC ba daidai ne, baya bisa ka'ida, ya saba kundin tsarin mulki, bai kamata ba kuma ba shi da wani tasiri."

Tinubu ya nada yan APC REC

A baya mun ji cewa akwai jiga-jigan jam'iyyar APC biyu a cikin sababbin Manyan Kwamishinonin hukumar zabe na INEC da za a nada.

Kamar yadda binciken Premium Times ya nuna cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kuma zabo wasu mutanensa cikin kwamishinonin zaben.

Etekamba Umoren (Akwa Ibom), Isah Ehimeakne (Edo) da Oluwatoyin Babalola (Ekiti) sune wadanda aka zabo don darewa wannan kujera.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng