Kano: Kujerar Majalisar Tarayya da Kotu ta Karbe Ya Dawo Hannun NNPP a Karshe
- Jam’iyyar NNPP ta yi galaba a kan APC mai mulkin Najeriya a Kotun daukaka kara a kan shari’ar zaben ‘dan majalisar Kumbotso
- Babban kotun ta ruguza nasarar da Mannir Babba Danagudi ya samu a Kotun korafin zabe, hakan ya na nufin murna zai koma ciki
- Alkalai sun yi hukunci cewa Hon. Idris Dankawu ne halataccen ‘dan majalisar Kumbotso, NNPP ta ce ta yi nasara a wasu mazabun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Kotun daukaka kara da ke garin Abuja ta yi zama a ranar Laraba, aka soke nasarar da kotun zabe ta ba Mannir Babba Danagudi.
Punch ta ce Mannir Danagudi da APC sun sha kashi a babban kotun domin an yi watsi da galabar da su ka samu a kotun korafin zaben Kano.
Kamar yadda hukumar INEC ta tabbatar a baya, kotun ta ce Hon. Idris Dankawu ne zababben ‘dan majalisar mazabar Kumbotso a jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkalai sun ba 'Dan majalisar NNPP gaskiya
Alkalai uku a karkashin jagorancin Tunji Oyebamuji su ka zartar da hukunci a karar da ‘dan majalisar na NNPP ya daukaka a kan APC.
Mai shari’a Tunji Oyebamuji ya ce kotun karbar karar zabe ta yi kuskure da ta maida hankali a kan takardar karatun Dankawu (NNPP).
Rahoton Solacebase ya ce Alkalan sun ce babu dalilin tsige ‘dan majalisar tun da bai gabatar da takardar shaidar wajen shiga takara ba.
Kotun da ke zama a birnin Abuja ta ce an yi kuskure wajen dogara da shaidan APC.
A karshe an ji an yi fatali da nasarar farko da Mannir Babba Danagudi ya samu saboda bai iya gamsar da kotu dalilin rusa zaben ba.
NNPP ta yi nasara a kujeru 4 a Kano
Hassan Sani Tukur wanda ya na cikin masu ba gwamnan shawara ya yi ikirarin NNPP ta yi nasara a kujerun Kiru/Bebeji da Wudil Garko.
Hadimin gwamnan na Kano ya ce jam’iyyar NNPP mai kayan dadi ta doke APC a shari’ar ‘yan majalisun Kumbotso da Dawakin Kudu/Warawa.
Majalisa: Kujerun NNPP su na dawowa
Haka aka yi a shari’ar Hon. Mukhtar Yarima mai wakiltar mazabar Nasarawa da ke jihar Kano bayan da farko kotun karar zabe ta karbe kujerarsa.
Da farko 'dan majalisar ya rasa kujerarsa ne a kan batun canjin suna da aka samu a takardun firamarensa, a kan haka APC ta kusa gaje matsaynsa.
Asali: Legit.ng