Jam’iyyar NNPP ta fitar da duk wadanda za su yi mata takaran zaben 2023 a jihar Kano

Jam’iyyar NNPP ta fitar da duk wadanda za su yi mata takaran zaben 2023 a jihar Kano

  • NNPP ta fitar da mutanen da za su yi mata takara a zaben majalisar dokoki da na wakilan tarayya
  • Jam’iyyar ta tsaida ‘yan takarar Sanatoci uku da mutum 64 da za su gwabza wajen neman majalisa
  • Rurum ya samu tikitin Kibiya/Bunkure, Jobe zai sake yin takara a Rimin Gado/Dawakin Tofa/Tofa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Jam’iyyar NNPP ta fitar da wadanda za su rike mata tuta a zabe mai zuwa a jihar Kano. An dauko duka ‘yan takarar ne ta hanyar cin ma maslaha.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa jagororin NNPP sun bukaci a samu maslaha tsakanin ‘yan takara daga kowace karamar hukuma da ke jihar Kano.

Idan ba a iya cin ma maslaha ba, za a shiga zaben fitar da gwani domin a fito da ‘yan takaran.

Kara karanta wannan

2023: Ƴan Takara 3,000 Ne Za Su Fafata Don Neman Tikitin Takarar Majalisun Jihohi a APC

Legit.ng Hausa samu hoton da ya nuna sunayen wadanda za su yi wa jam’iyyar takara a 2023. A majalisar dokokin jiha, akwai gurabe hudu da ba a cike ba.

Har yanzu ba mu da labarin wadanda za su yi wa NNPP takarar ‘dan majalisar dokoki daga mazabun Warawa, Rano, Rimin Gado/Tofa da Makoda a badi.

A takarar ‘dan majalisar wakilan, kusan jam’iyyar ta cike duka kujeru 24 da ake da su. Kujerun da mu ke tantama su ne na yankin Ajingi/Gaya/Albasu da Bichi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jam’iyyar NNPP
Masu takara a NNPP Hoto: Salisu Hotoro
Asali: Facebook

Sanannun fuskoki za su dawo?

Wasu daga cikin wadanda su ka samu tikitin NNPP sun hada da: Mukhtar Umar, Idris Dankawu da Barr. MB Shehu a yankin Taurani, Kumbotso da na Fagge.

Abdulmumin Jibrin ya samu tikitin Kiru/Bebeji, Yushau Soja shi ne zai sake takara a Tudun Wada/Doguwa, Kabiru Rurum zai sake jarraba sa'arsa a 2023.

Kara karanta wannan

Sai dai a buga, Sanata mai-ci ya ce ba zai janyewa Gwamna takarar Majalisa a APC ba

Tijjani Jobe zai nemi ya koma kujerarsa, Nasiru Sule Garo ya samu tikitin Kabo/Rano, haka zalika Aliyu Madakin Gini shi za a tsaya domin ya wakilci yankin Dala.

Shehu Na Allah ya samu tikitin Kura/Garun Malam da Madobi jim kadan bayan ajiye mukamin da yake kai na kwamishina a gwamnatin Abdullahi Ganduje.

A 2023 Garba Diso zai sake yin takara a Gwale, Sagir Koki ya samu tikitin birnin Kano a NNPP.

Majalisar dokoki

Masu takarar majalisar jiha sun kunshi: Hafizu Sani Ɗan daji (Dambatta), Yusuf Aliyu (Nassarawa), Sarki Aliyu Daneji (KMC), Lawal Husseini (Dala).

Kabiru Dahiru Sule (Tarauni), Aminu Sa'ad Ungogo (Ungogo), sai Abdulhamid A. Minjibir (Minjibir).

Takarar Sanatoci

Ku na da labari Ibrahim Shekarau ya samu tikitin Kano ta tsakiya. Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila shi ne ‘dan takarar Sanatan NNPP a kudancin jihar Kano.

A Arewacin Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ne zai rikewa NNPP tutan Sanata a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Saura kwana 10 zabe, an shiga yamutsi a PDP game da wanda za a tsaida takara

Asali: Legit.ng

Online view pixel