Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Zaben Sanatan PDP, LP a Arewa, An Bayyana Mai Nasara
- Sanata Ireti Kingibe ta jam’iyyar LP ta yi nasara a kotun daukaka kara bayan daukar lokaci mai tsawo ana shari’a
- Kotun yayin yanke hukuncin, ta yi fatali da karar Sanata Philip Aduda na jam’iyyar PDP a mazabar birnin Abuja
- Kotun ta yanke hukuncin ne ta manhajar ‘Zoom’ a yau Laraba 1 ga watan Nuwamba a birnin Abuja
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin Tarayya ta tabbatar da nasarar Sanata Ireti Kingibe ta jam’iyyar LP a Abuja.
Kotun har ila yau, ta yi fatali da korafe-korafen Sanata Philip Aduda na jam’iyyar PDP kan kalubalantar zaben Sanata Ireti mai wakiltar mazabar birnin Abuja.
Wane hukunci kotun ta yanke a Abuja?
Kotun yayin yanke hukuncin a yau Laraba 1 ga watan Nuwamba ta yi fatali da karar Aduda inda ta ce ba shi da gamsassun hujjoji, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin sanar da sakamakon zabe a watan Faburairu, baturen zaben na birnin Abuja, Farfesa Sani Saka ya ayyana Kingibe a matsayin wacce ta lashe zaben.
Saka ya bayyana cewa Kingibe ta samu kuri’u 202,175 yayin da Aduda ya samu kuri’u 100,544 inda ya zamo na biyu a zaben.
Wane korafi Sanata Aduda ya yi a kotun Abuja?
Daga bisani Aduda ya kalubalanci sahihancin zaben da cewa an tafka magudi inda ya durfafi kotun kararrakin zabe, The Whistler ta tattaro.
Lauyoyin Aduda sun yi zargin cewa an bayyana Kingibe a matsayin wacce ta lashe zabe tun kafin a kammala harhada sakamakon wasu mazabu.
Yayin da Kingibe ta bakin lauyoyinta ta bukaci kotun ta yi watsi da korafe-korafen Aduda saboda rashin hujjoji.
Kotun zabe ta yi hukunci kan zaben sanatan APC
A wani labarin, kotun sauraran kararrakin zabe a jihar Plateau ta yi hukunci kan shari’ar zaben sanata a mazabar Plateau ta Tsakiya.
Kotun ta tabbatar da nasarar Sanata Diket Plang na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe.
Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam’iyyar PDP, Yohanna Gotom saboda rashin gamsassun hujjoji.
Asali: Legit.ng