Kotun Zabe Ta Yi Hukunci Kan Sahihancin Zaben Sanatan APC a Jihar Arewa, Ta Fede Komai

Kotun Zabe Ta Yi Hukunci Kan Sahihancin Zaben Sanatan APC a Jihar Arewa, Ta Fede Komai

  • Sanata Diket Plang na jam'iyyar APC ya samu nasara a kotun sauraran kararrakin zabe da ke jihar Plateau
  • Yohanna Gotom na jam'iyyar PDP na kalubalantar sahihancin zaben Plang na jam'iyyar APC a zaben da aka gudanar a watan Faburairu
  • Alkalin kotun, Mai Shari'a, Omaka Elekwa yayin yanke hukuncin, ya yi fatali da korafin Gotom inda ya ce ba shi da hujjoji gamsassu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Kotun sauraran kararrakin zabe a jihar Plateau ta tabbatar da nasarar Sanata mai wakiltar Plateau ta Tsakiya, Diket Plang.

Plang wanda ke jam'iyyar APC ya samu nasarar ce a yau Laraba 1 ga watan Nuwamba, Tribune ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan zaben sanatan Kogi ta tsakiya

Kotun zabe ta yi hukunci kan zaben sanatan APC a Plateau
Kotun ta yanke hukunci kan zaben Sanata Plang na APC. Senator Diket Plang/Facebook.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke a Plateau?

Yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a, Omaka Elekwa ya yi fatali da korafin Yohanna Gotom na jam'iyyar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Elekwa ya ce korar karar ta zama dole saboda tarun hujjoji da ke nuna sahihancin zaben da kuma sakamakon da hukumar INEC ta tabbatar.

Kotun ta kuma tabbatar da cewa sakamakon zabe daga mazaba 34 a yankin Gagdi da ke karamar hukumar Kanam ingantattu ne.

Mene alkalin kotun ya ce kan shari'ar zaben?

Har ila yau, kotun ta kara da cewa baturen zaben, Farfesa Sunday Dabi ba shi da karfin ikon soke sakamakon zaben, cewar Premium Times.

Elekwa ya kuma tabbatar da cewa jam'iyyar PDP ba ta dauki nauyin Yohanna na jam'iyyar yadda ya kamata ba inda ta ce ba shi da ikon kalubalantar zaben.

Kara karanta wannan

Kotun koli: Jerin sunayen sanatoci da jiga-jigan PDP da su ka yi watsi da jam'iyyar bayan faduwar Atiku

Yayin martaninshi, Sanata Plang ya yabi hukuncin kotun inda ya ce hakan ya kara masa imani da bangaren shari'a a kasar.

Kotun zabe ta tabbatar da nasarar Sanata Wamakko

A wani labarin, kotun sauraran kararrakin zabe a jihar Sokoto ta tabbatar da nasarar Sanata Aliyu Wamakko a matsayin halastaccen zababben sanata.

Wamakko wanda dan jam'iyyar APC ne ya samu nasarar kan abokin hammayarsa na jam'iyyar PDP, Mannir Dan'iya.

Kotun har ila yau, ta yi fatali da korafin tsohon mataimakin gwamna, Mannir Dan'iya na jam'iyyar adawa a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.