Tinubu Zai Kashe Naira Biliyan 1.5 Wajen Sayo Motocin Uwargidar Shugaban kasa
- Da zarar majalisar tarayya ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kudin 2023, za a iya kashe fiye da karin Naira Tiriliyan 2.1 a bana
- Kundin kasafin kudin ya na dauke da motocin sama da Naira Biliyan 1 da za a saya domin amfani uwargidar shugaban Najeriya
- Gyaran wurin kwanan Mai girma shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a fadar Aso Rock zai ci wa gwamnati Naira biliyan 6
Abuja - Gwamnatin tarayya ta na shirin batar da N1.5bn a kan motocin da za a rika amfani da su a ofishin uwargidar shugaban Najeriya.
Rahoton Premium Times ya nuna za a kashe wadannan makudan kudi ne idan an amince da kasafin kudin da ke gaban majalisar tarayya.
Shugaba Bola Tinubu ya aikawa majalisa kundin kwarya-kwaryan kasafin kudin 2023, hakan zai bada damar kashe karin wasu N2.17tr.
Da gaske gwamnatin Najeriya ba ta da kudi?
Yayin da gwamnatin Tinubu ta ke ikirarin babu kudi a kasa, sai aka ji cikon kasafin da aka yi ya na kunshe da kudi na sayen motoci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga tashi da man fetur ya yi da 400% a sakamakon janye tallafi a karshen watan Mayu, kayan abinci su na ta cigaba da kara tsada.
Tinubu: Aso Rock za ta lakume N28bn
Rahoton ya ce kundin tsarin mulki bai san da ofishin matar shugaban kasa ba, wannan ba zai hana a batar da N1.5bn a kan motocin ta ba.
Baya ga motocin Sanata Remi Tinubu, za a batar da N2.9bn domin sayen wasu manyan motoci da za a rika amfani da su a fadar Aso Rock.
Za a gyara wurin kwanan Tinubu da Shettima
A cikon kasafin kudin na bana kuma ake shirin kashe N4bn wajen gyara inda shugaban kasa yake zama, watanni biyar da canjin gwamnati.
N2bn za su tafi a gyaran wurin da mataimakin shugaban kasa ya ke zama a Aso Rock.
Shisshigin Seyi Tinubu a gwamnati
Jiragen da ke fadar shugaban Najeriyan za su ci N12.5bn da sunan gyara. Kwanaki Seyi Tinubu ya hau wani daga ciki domin zuwa wasan Polo.
Ana da labari cewa an gano mutane su na kurdowa Aso Rock idan ana taro, daga yanzu babu wanda zai shigo FEC sai da izinin shugaban kasa.
Bayan ya ga hoton yaronsa a taron Ministoci, shugaban kasa ya bada umarni a tabbata ba a bude kofar Aso Rock ga wanda ba a gayyata ba.
Asali: Legit.ng